Abubakar Abba" />

Dalilin Da Ya Sa Nijeriya Ba Ta Iya Fitar Da Rogo Yanzu

Akwai abubuwa da dama dake takawa Nijeriya birki wajen fitar da Rohonzuwa kasuwannin kasashen duniya wadanda suka hada da, tsadar noma Rogon da har yanzu ake fuskanta a kasar, karancin kayan aikin na zamani na noman Rogon da kuma dabarun habala noman sa da sauran su.

Hakan ne ya sanya a Cibiyar gudsnar da bincike ta samar da ingantacciyar Jijiyar Rigo ta kasa (NRCRI) dake a yankin Umudike cikin jihar Abiya suka yi bayani a yayin da wata tawagar kungiyar manoman kimiyya ta Biosciences data fito daga Afrika suka kai ziyara a Cibiyar don yin dubi kan irin bincike-binciken da Cibiyar keyi a fannin noman Rogo a Nijeriya.

Mataimakin Darakta na Cibiyar Dakta Kenneth Ekwe kuma mai kula da sashen yada labarai da hudda da jama’a na Cibiyar ya zagaya da tawagar cikin Ciiyar da kuma nuna masu irin bincike-binciken da ake gudanrwa a Cibiyar.

Ya sanar da cewa, tun lokacin da aka kafa Cibiyar, ta jagoranci gudanar da bincike kan nau’ukan Rogo guda 43, wadanda kuma cuta bata kama su kuma ko ba a kasar nan ba, za’a iya noma su.

Ya kara da cewa, akwai kuma kalubalen dake karyawa manoman Rogo kwarin gwaiwa wajen yin kasawancin sa cikin hida, indanhakan yake sanyawa suna kasancewa cikin fatan bukatar sa a kasuwannin duniya don su samu riba ma yawa.

Ya kuma nuna damuwar sa kan yadda ake samun chanje-chanje kan tsare-tsaren noman Rogo a kasar, inds ya yi nuninda cewa, hakan yana kara shafar noman sa da kuma fitar dashi zuwa kasar waje, inda ya yi nuni da cewa, farashin Masara a cikin gida Nijeriya yana gogayya da farashin Rogo.

Ya sanar da cewa, manoman Rogo a kasar nan, basi da karfin da zasu iya fadada noman Rogon, musamman saboda rashin wadatattun kudade da kayan aiki, inda a kara da cewa, akwai kuma matsalar rashin yanayi mai kyau da ba’a samar ba.

Dakta Ekwe ya ci gaba da cewa, idsn Nijeriya ta baiwa fannin kulawar data dace, musamman ta hanyar yin amfani da kimiyya noman na Rogon, zai iya tafiya kada da kafada da mai wajen tarawa Nijeriya kudade musaya na kasar waje.

Ya yi nuni da cewa, akwai bukatar a kara bunkasa noman Rogo a kasar da kuma samar da magungunan dasu kare shi daga kamuwa da cututtuka.

Dakta Ekwe ya ci gaba da cewa, idsn Nijeriya ta baiwa fannin kulawar data dace, musamman ta hanyar yin amfani da kimiyya noman na Rogon, zai iya tafiya kada da kafada da mai wajen tarawa Nijeriya kudade musaya na kasar waje.

Exit mobile version