Connect with us

LABARAI

Dalilin Da Ya Sanya Muka Janye Yajin Aikin Da Muka Kuduri Aniyar Shiga – Likitoci

Published

on

Kungiyar Likitoci ‘yan gida, (NARD), sun bayyana dalilin da ya sanya suka janye yajin aikin kasa bakidaya da suka yi niyyan farawa, wanda zai kai ga kara tabrbrewan halin da ake ciki a asibitocin kasarnan.

Kungiyar ta ce, hukumomin asibitin koyarwa na Jami’ar Jos, sun mayar da ‘yan’uwanmu likitocin da suka sallama kwanan nan, wanda hakan shi ne babban abin da ya fusata mu.

Suka kuma ce, sun yi farin ciki da matakan da gwamnatin tarayya ta dauka kan yarjejeniyar da suka cimma a tsakaninsu da gwamnatin.

Shugaban Kungiyar da Sakatarensa, Dakta Ugochukwu Chinaka, ne suka fadi hakan cikin sanarwar da suka fitar bayan kammala taron gaggawan da kungiyar ta kira a Abuja, ranar Lahadi, suka ce sun dauki wannan matakin ne domin kare sashen na lafiya da kuma samar da yanayin tattaunawa don warware matsalolin cikin ruwan sanyi.

Kungiyar kuma ta yi roko ga Shugaba Buhari, da ya sanya hannu kan dokar shirin bayar da horo ga likitocin ‘yan kasa, don magance duk wasu matsaloli na likitocin na gida.

Ya ce, “Mun yi amanna da tattaunawa mai ma’ana. Hakan ne ya sanya muka shiga cikin tattaunawar sosai, za kuma mu bi duk matakan da suka kamata domin warware dukkanin matsalolin cikin ruwan sanyi, domin tausaya wa majinyatan da ke cikin zukatanmu.”

Kungiyar ta kirayi daukacin ‘ya’yanta da su yi aiki dare da rana domin taimaka wa majinyata da kuma daukaka martabar sashen na lafiya.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: