A kokarinta na samar da mafita, ga ‘yan gudun hijira, gwamnatin tarayya ta kaddamar da aikinta na tallafa wa aikin aikin noma da ake kira ‘REHAEP’ ga ‘yan gudun hijirar da ke zaune a Jihar Filato, a sansaninsu na yankin Kpwasho a Karamar Hukumar Bassa ta jihar.
Har ila hau, aikin hadaka ne tsakanin hukumar kula da bakin haure da ‘yan gudun hijira ta kasa da kasa (NCFRMI) da kuma ma’aikatar aikin noma da samar da wadataccen abinci.
- Sabon Matakin FOCAC Na Jagorantar Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Wajen Zamanintar Da Al’umomminsu
- Dalilin Da Ya Sa Makiyaya Suka Tafka Asarar Shanu Sama Da 1,000 A Taraba
Kwamishinan hukumar, Tijjani Ahmed ya bayyana cewa; an ware gona mai fadin kadada 150, domin gudanar da wannan aiki, inda ya kara da cewa, ‘yan gudun hijira 300 za a tallafawa da kayan aiki da kuma tallafin kudi.
Haka zalika, Ahmed ya kara da cewa; su ma masana’antu masu zaman kansu, za su taimaka wajen tabbatar da ganin an yi girbin amfanin gonan da ‘yan gudun hijirar suka noma, wanda hakan zai taimaka wajen kara samar da wadataccen abinci a fadin kasar nan baki-daya.
Ya ci gaba da cewa, an wanzar da wannan aiki na gwaji a Jihohin Nasarawa da Borno, wanda kuma aka shirya fadada shi zuwa sauran jihohin kasar nan, har zuwa shekara biyar.
A cewar Ahmed, za a shuka Irin noma kamar na Shinkafa, Masara, Dawa, Alkama da sauransu a cikin wadannan kadada 150.
Sanna kuma ya ce, ma’aikatar aikin noma da samar da wadataccen abinci, za ta samar da kayan aiki, domin noma hekta 150, inda kuma hukumar NCFRMI za ta samar da tallafin kudade ga ‘yan gudun hijirar.
Ahmed, wanda Darakata ne a hukumar; Fatima Mamman Daura ita ce ta wakilce shi tare da bayyana cewa, hukumar ta kuma yi hadaka da rundunar tsaron farin kaya ta NSCDC da ke bai wa manoma kariya,
Shi kuwa gwamnan jihar, Caleb Muftwang a nasa jawabinn ya ce, ya kamata manoma a jihar su rika yin noma mai yawa, inda ya kara da cewa; gwamnatinsa za ta tallafa wa wadannan ‘yan gudun hijira.
Muftwang, wanda shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa na jihar ‘PLASSIMA’, Mista Sunday Audu ya wakilta a wajen taron ya ci gaba da cewa, gwamnatinsa za ta tabbatar da an mayar da ‘yan gudun hijirar ga matsugunansu tare da magance kalubalen karatun ilimin boko na ‘ya’yansu.
A cewar tasa, a yanzu haka akawai hadakar da ake ci gaba da yi da jami’an tsaro da rundunar tsaron farin kaya ta NSCDC, domin karfafa tsaro a gonakan manoman ta yadda za su yi nomansu ba tare da jin wani tsoron harin ‘yan bindiga ba.