Connect with us

ADABI

Dalilin Himma Ta Ga Noma Shata Ya Yi Ma Ni Wakoki -Marigayi Garba Dan Ammani Funtuwa

Published

on

Wannan wata tsohuwar hira ce da aka yi cikin 2003. A ranar Lahadi 10/8/2003 Dokta Aliyu Ibrahim Kankara, fitacceen marubucin littafin Dokta Mamman Shata Katsina ya yi tattaki ya kai ma Alhaji Garba Dan Ammani Funtuwa ziyara, inda mawallafin ya nemi jin ta bakin yallabai game rayuwarsa da sana’arsa. Ya kuma nemi ya ji dangantakarsa da marigayi zakin mawaka, Shata Katsina. Ga dai yanda hirar ta kasance.

Aliyu Kankara: Ranka ya dade, a ina aka haifeka, kuma wanene magabacinka?

Dan Ammani: An haife ni a garin Funtuwa. Sunan mahaifina Alhaji Ammani. Shi, manomi ne kuma dan kasuwa. Ya taba siyasa ta NPC.  Muna da yawa a gidanmu, wadanda mahaifinmu ya haifa.

Aliyu Kankara: Ranka ya dade, zancen karatu fa, an yi koko?

Dan Ammani: Na yi karatun allo da ina karami a nan gaban mahaifina a Funutuwa. Na halarci makarantar Firamare ta garin Funtuwa daga shekarar 1944 zuwa 1949. Daga nan na zarce makarantar Midil watau Middle  ta Katsina daga shekarar 1949 zuwa 1952. Sai na tafi kwalejin horas da ‘yansanda ta Kaduna, da ake kira Police School (College) na gama. Sai kuma na tafi na yi karatun Kananan Hukumomi, watau a turance District Scribe (Malamin Hakimi) Dan a kammala na dawo gida Funtuwa, sai kuma na ci-gaba harkokin kasuwanci na saye da sayarwa da kuma noma.

Aliyu Kankara: Ranka ya dade, na fahimci akwai kyakkyawar alaka a tsakaninka da Shata na Bilkin Sambo. Har ma ya yi maka waka. Yaya abin yake?

Dan Ammani: Na san Shata tun wajen shekarar 1960 lokacin da ya dawo Funtuwa da zama. Na san yana yawan zuwa wajen mahaifin mu Alhaji Ammani. Mahaifina ubangidansa ne. Kuma akwai dangantaka mai kyau a tsakaninsu. Ya kan zo wajen sa domin neman shawara na idan yana son ya yi wani abu. Ka san Shata yana da biyayya da girmama na gaba, ballantana a ce mutum ubangidansa ne. To yana yawan girmama mahaifina. Wannan ya fara sada ni da shi har muka rika yin abotaka. Na fahimce shi sosai, shima ya fahimce ni.

Bayan mahaifina ya rasu sai muka ci-gaba da yin amintaka tare. Idan ka ga na ba Shata kudi, to ya ga ta tsure ba shi da ko kwabo za ya zo in ba shi. Ko kuma ya zo neman albarushi idan za ya tafi daji yawon halbi.

Amma dai, a ce in dauki kudi in ba Shata don ya yi mani waka, gaskiya ban taba yi ba. Shi kuma bai taba jarraba ya ce in bas hi kudi ya yi mani waka ba. Ni ban taba ba shi ko kwabo ba kafin ya yi mani waka, baya ga ‘yan kudin cefane da na kan dan tsakura masa idan ya zo nema. Wannan kuwa ai ba wata kyauta b ace ta ku-zo-ku-gani, ga mutum dai kamar Shata.

Aliyu Kankara: Yaushe ya yi maka waka, kuma minene sala?

Dan Ammani: Asalin waka ta na kira taron manoma a gona ta da ke kan hanyar Sokoto cikin 1985.

Aliyu Kankara: Zamanin mulkin Janar Muhammadu Buhari ke nan?

Dan Ammani :E, kwarai da gaske. To, shima Shata ya zo don na kira shi tunda shi ma manomi ne. Duk wanda ka sani ya amsa sunan sa a Najeriya wajen aikin noma ya zo wurin. Mun yi taro. A dalilin wannan taro ne ya yi ma ni wakoki biyu, cikin 1985.  Yana cewa: ‘Akwai kayan aiki gun Garba Dan Ammani’,  da kuma wadda yake cewa: ‘Akwai aiki gun Garba Dan Ammani’

Aliyu Kankara: To akwai aiki a wurin Garba Dan Ammani din koko dai zuga ce irin ta maroki?

Dan Ammani: E, a lokacin na yo odar kayan aiki. Kamar su Taraktocin noma ashirin (20) daga Kasar Faransa watau  France. Ko minene, in dai ya danganci aikin gona, to za ka same shi a gona ta. Har da wanda ma ba ka zato.

Aliyu Kankara: Ina tammanin kamar ba su kadai ba ne (wakokin), za su kai kala hudu (4)

Dan Ammani: Ba shakka daga baya ya yi wasu wakokin amma nima saidai aka rika fada mani don ba a gabana yake yin su ba.

Aliyu Kankara: Ranka ya dade na ga a saman falon ka ko’ina ga hotunan ku nan, kai da Janar Muhammadu Buhari a lokacin yana shugaban Kasa. Ko akwai wata alaka a tsakanin ku?

Dan Ammani: Janar Muhammadu Buhari babban amini ne, kuma masoyi. Shi da kan sa said a ya zo gona ta wadda aka yi wancan taro. Sannan kuma yana zuwa Funtuwa waje na. Na kan je wajen sa duk sa’adda ya yi wata sabga a gidansa. Dangantakar mu mai karfi ce. Ko wani abu ake so ya yi a Funtuwa ko ma wani wuri, in dai ya shafi Katsina, to a kan hada da ni don an san ba ya yi mani gardama.
Advertisement

labarai