Connect with us

KIWON LAFIYA

Dalilin Kafa Gidauniyar Kiwon Lafiya Ta Mata Su Duba Mata —Dakta Maryam

Published

on

DAKTA MARYAM ABUBAKAR ita ce shugabar Gidauniyar kiwon lafiya ta mata su duba mata wadda a turance ake kira “Women For Women”. A hirarta da ABUBAKAR ABBA ta bayana dalilin da ya sa suka kafa gidauniyar reshen jihar Kaduna.
Yaushe ki ka kafa gidauniyar?
Yau tana da shekara hudu da kafuwa kuma dalilin da ya sanya na kafata shinen nayi aiki a wani asibiti a jihar Kano a lokacin dana yi aiki a wani asibiti dake cikin karamar hukumar Kiru a cikin jihar sai naga idan mata sunzo asibitin a duba su sai su dinga rabewa basa son namiji ya duba su sai kafa wannan gidauniyar ta mace ta duba mace saboda ba dukkan mace ke son namiji yaga tsiraicin ta ba. Kuma akwai matar data samu zubar ciki a lokacin da tazo ayi mata wani aikin ciki, saboda taki likitan namiji ya dubata harta samu matsala a mahaifarta, munce wa matar ai ciwo ne kuma larurace, amma dana zauna na duba nace wannan ya zamo mana kalubale mu mata da muke aiki a asibitin shi yasa na kafa wannan gidauniyar don taimakawa mata masu fama da larurori.

Wadanne manyan nasarori ki ka samu tun lokacin kafata?
Gaskiya an samu nasarori, saboda har yanzu wuraren dana gaya maka, mata suke duba mata in har kaga likita namiji ya shigo toh, sai in ba mata likitoci ko kuma matar tana fama da ciwo ne mai babbar matsalar gaske zai sanya namiji likita ya duba ta, toh dalilin da ya sanya ke nan bayan na dawo Kaduna, sai naga in muna son mu tafiyar da wannan abin, muma sai muka kafa wannan asbitin nawa na Fatima Clinic dake anguwar Dosa Kaduna, inda muke duba mata da kuma karbar haihuwa kuma har na fara jin wasu ‘yayan gidauniyar dake jihar, suma suna baude irin wannan asibitocin nasu, indsa sukje duba mata kuma har hakan ya sanya wasu asibitocin masu zaman kansu dake jihar sun fara kwai-kwayar mu wadanda ma na maza ne, sun fara ckawo mata yanzu, inda mace zata duba mace, inda ko kai miji ma, ba zaka san larurar da matar ka take ciki ba, domin mace ‘yar uwarta ce zata dubata, zata saki jiki sosai, domin kamar tazo ace tazo asibiti kuma namiji ne zai sanya mata hannu a gabanta, sai tace mashi ta warke. Akwai wadanda zasu kai shekara goma suna fama da matsala amma basu san ko wacce kwayar cuta suka kamu da ita ba, musamman wadda ake dauke a bandaki, amma su kasa zuwa a duba su. Haka kamar matsalar cutar Daji ta Nono, idan mata masu fama da larurar, sukazo asibiti, namiji ne zai duba su, amma yanzu yawanci mata ne ke duba su, haka kamar in munje wa’azi, muna wayarwa da junan mata kai akan cutar ta dajin ta Nono inda ba sai mace ta tube rigar ta ba, muna yi masu misali akan yadda zasu dinga duba Nonon su. A cikin ikon Allah, sai naga abin nawa yana ta karbuwa domin yanzu mata sun fara gane alomin cutar ta dajin Nono.

Amma sai kuma aikin naku yafi tsayawa a cikin birni, kuna tunanin fadada shi zuwa yankunan karkarar jihar?
Ah! akwai kamar akwai wani kauye danaje kwanan baya, inda nayi Magana da matan kauyen suka gaya mini su basu da ma asibiti. A soaboda haka akwai abinda muke kokarin mu shiryawa wannan kauyen kuma insha Allahu zamuje, kuma tuni mun fara tattaunawa da mutanen kauyen. Alhamdullahi, muna da yawan mata a matakan lafiya na farko saboda daukare aikin da gwamnatin jihar ta yi a kwanan baya.

Wanne kira zaki yi ga iyayen don su dinga baiwa ‘yanyan su mata kwarin gwaiwar shiga aikin kiwon lafiya?
A kullum muna yin irin wannan kiran kuma kamar yadda naji malamai suna yin wa’azi akai domin idan mace ta koyi aikin kiwon lafiya, zata taimakawa harda iyalanta da ‘yan uwanta tana dakin ta zata iya taimakawa ko makwabtan ta ko kuma alumma baki daya.
Wadanne manyan kalubale gidauniyar take fuskanta?
A gaskiya akwai su da yawa saboda wasu na ganin akan me za ‘ace sai dai mace ta duba mace bayan kuma addini ma ya halasta a bar mace ta duba mace in har ta san abinda takeyi sai dai in bata sani ba saboda maza likitoci suna ganin kamar zamu kwace masu aikinsu, amma alhali ba haka bane. Kuma muna son matan mu musamman na Arewa su samu sake wani ma sai yace ai ana son a kawo addini a ciki, bayan a cikin mu akwai Kiristoci da Musulmai wadanda suma sunfi son mata su duba su.

Baki kiyi maganar kalubalen kudi ba ko baku da wannan matsalar?
Muna samun kudaden mu daga wasu wurare amma gwamnati bata bamu Allah ne yake taimaka mana kuma Alhamdulillahi, inada miji mai ganewa kuma tun filazal, yanada wannan abin domin duk gudunmawar dana ke so yana yi mini har ila yau, ni Kande ce na girma a cikin maza biyar suna taimaka mini kuma bayana mata ne nan nake samun kudi na.

Kwanan baya gidauniyar ku ta yiwa wasu masu fama da Fabiroyedn me ya baku tunanin yin hakan?
Dalilin shine, ana fama dashi domin zakaga anzo asibiti ciwon da bafi a kashe naira 20,000 za’a kashe ba amma basu da hali shi yasa muka yi masu don mu taimaka. Haka fannin ciwon hayaniya zakaga an kawo Yaro asibiti idan aka cewa baban Yaron za’a yi masa aiki sai yace baida hali amma da sukaji mun bayar da sanarwar zamu yi akin cutar kyauta ga muatne ashirin sai muka samu mutane sama da hamsin sukazo, karfin mu kuma na mutane ashirin ne kuma muka yiwa asshirin din kyauta sai sauran suka fara biyan rabi, wasu ma naira dubu biyar suka biya muka karba muka yi masu.

Kamar yawan mutane nawa ne suka amfana gaba daya?
Yara ‘yan kasa da shekara biyar da maza magidanta su sittin aka yiwa aikin.

Kwanan baya gidauniyar ku taje gidajen marayu ta rabar da abinci menene manufar hakan?
Anyi hakan ne don a taimakawa marasa galihu kuma munyi hakan ne don zagayowar bikin ranar duniya ta yara yadda kada yaran suga kamar an mayar dasu saniyar ware daga cikin alumma yadda suma zasu san cewar ba’a manta dasu ba.

Ganin cewar 2019 na kara karatowa, ko akwai wasu shirye-shiye na musamman da gidauniyar ku ke da kudurin yi?
So sai kuwa, domin akwai abubuwan da muka sanya a gaba a watan Satumba mai zuwa zamu fito da wani aiki wanda zamu baiwa Kaduna mamaki in sha Allah.

Yaushe kika kafa Fatima Clinic ?
An kafa ne daga baya, inda mukace a kafa asibitin mata su duba mata shi ya sanya muka kafa don mu zama babban misali ba wai kawai cewa mutane su kafa ba, inda a yanzu asibitin yanada shekara biyu.

Ya kike ganin zuwan marasa lafiya musamman mata zuwa asibitin?
Gaskiya na fara jin mata suna kiran asibitin da sunan asibitin mata, amma maza ma suna zuwa, akwai karbuwa fiye da yadda nake tunani domin musamman mata daga wasu anguwanni dake cikin Kaduna suna zuwa don a duba lafiyar su.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: