A makon da ya gabata ne, Hukumar Bunkasa Noma da Raya Gonaki ta kasa NALDA, ta shelanta cewa, tana shirin daukar masu digiri har matasa 30,000 aiki a daukacin fadin Nijeriya.
A cewar Hukumar, gwamnatin tarayya ta kuma sanya hannun amincewa a dauki matasan domin bunkasa fannin aikin noma da kuma wadanda za a dauka domin inganta dabarun kimiyya.
Shugaban Hukumar Paul Ikonne ya bayyana haka a Abuja, inda ya kara da cewa, daukar matasan ya zama wajibi domin su ne za su yi aikin gwajin ni’imomi da albarkar kasar noma, tare da bayar da shawarwari ga manoma a karkashin shirin bunkasa matasa manoma da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar a watan Nuwambar shekarar 2020.
A cewar Shugaban Hukumar Paul Ikonne tun farko dama idan ana so a cimma nasarar bunkasa noma, sai an yi bincike da gwajin kasar noma idan ta cancanci a shuka abin da ake bukatar shukawa a wurin ko kuma a san me ya kamata a shuka a gonar.
Paul Ikonne wanda ya sanar da hakan a hirarsa da manema labarai dangane da ayyukan dake gaban hukumar sa ya ci gaba da cewa, ba za mu iya samar wa kasar nan wadataccen abinci ba, har sai mun fahimci irin kowace kasa ko gonar da ya kamata a shuka kowane nau’in abinci tukunna.
Shugaban Hukumar Paul Ikonne ya kara da cewa, a kan haka ne Shugaban kasa Muhammau Buhari ya amince Hukumar ta dauki matasa 30,000 domin yin aikin nazarin kasar gonaki da kuma yin gwajin irin shukawa a wurin da ya kamata a shuka abin da ya dace a shuka a wurin har a samu sakamakon amfani gona sosai, inda ya yi nuni da cewa, wannan kuwashi ne tushe da ginshikin noma baki daya a Nijeriya.
A cewar Shugaban Hukumar Paul Ikonne, kwanan nan ne wannan hukuma ta kaddamar da shirin bunkasa Matasa manoma, musamman domin daukar matasa 1,000 daga kowace karamar hukuma 774 aikin gona a kasar nan, inda ya kara da cewa, za a bai wa masu digiri din horo na makonni biyu.
Shugaban Hukumar Paul Ikonne ya kuma sanar da cewa, za a rika biyan kowanen su naira 500 a duk sakamakon gwaji daya na kasar noman da ya dauko.
A wata sabuwa kuwa, mataimakin gwamnan jihar Kano Nasiru Gawuna ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta horas da manoma 20,000 a jihar.
Gawuna ya ce gwamnati ta horas da manoman ne ta hanyar shirin ta na APPEALS da gwamnati ta kirkiro a shekaran 2016.
Ya ce gwamnati ta tsaro wannan shiri ne domin inganta aiyukkan noma ta hanyar wayar koyar da su sabbin da dabarun noman zamani, samar da aiki da abinci domin inganta tattalin arzikin kasa, inda ya kara da cewa, gwamnati za ta horas da manoman shinkafa, alkama da tumatir sama da 10,000 dabarun noma na zamani da kasuwanci.
A cewarsa, daga cikin wannan yawa shirin ya horar da manoma 6,344 sannan shirin ya kuma horar da mata, matasa da masu fama da nakasa a jikinsu 1,700 kiwon kifi da kaji, inda ya kara da cewa, bayan an kammala horas da manoma gwamnati za ta basu kudaden jari da kayan aiki domin su fara sana’a.
Shi ma a nasa jawabin, Manajan shirye-shirye Dakta Salisu Garba ya ce gwamnati ta kirkiro wannan shiri ne tare da hadin gwiwar babban bankin duniya, inda Garba ya ci gaba da cewa, tun bayan kirkiro shirin a shekarar 2016 ake gudanar da irin wannan horaswa a wasu jihohin kasar nan.
Shi kuwa, Kwamishinan kananan hukumomi na jihar Murtala Sule-Garo ya ce, Gwamnatin jihar Kano ta raba injinan banruwa 5,000 wa manoma domin inganta aiyukan noman rani a jihar, inda Sule-Garo ya ce gwamnati ta tura ma’aikatan noma don taimakawa manoma da koyar dasu dabarun aikin gona na zamani a duk kananan hukumomi 44 dake jihar.
Gwamnatin Tarayya Za Ta Cigaba Da Samar Da Ingantattun Irin Karo – Minista Shehuri
Gwamnatin Tarayya ta shelanta cewa, za ta ci gaba da...