Jam’iyyar PDP, a Kano ta ce ba za ta shiga a fafata da ita ba a zaben kananan Hukumomin Jihar Kano da ke tafe ba. shugaban kwamitin riko na jam’iyyar ta PDP , DanLadi Abdulhamid ne ya bayyana haka ya yin taron manema labarai a ofishin jam’iyyar dake Jihar Kano.
Danladi Abdulmumin ya yi zargin cewa an fitar da kudaden da suka wuce kima wajen yin zaben, sannan kuma suna tsoron haifar da rikici yayin zaben. Ya ce babu yadda za yi su shiga zaben da tuni Gwamnan Kano Ganduje ya rubuta wadanda za su ci.
Ya kuma ce Gwamnati ta ware kudi kimanin naira Biliyon biyu da miliyon dari uku kan zaben da sun riga sun san su za su baiwa kansu.
Tuni dai Hukumar zabe mai zaman kanta ta Jihar Kano ta sanar da watan Janairun badi a matsayin watan da za ta gudanar da zaben kananan Hukumomi da na kasiloli a fadin Jihar Kano