Abubakar Abba" />

Dalilin Wani Kamfanin Shinkafa Na Samar Wa Mutane 5000 Aiki

Kamfanin Casar Shinkafa na Zangon Kangiwa a cikin jihar Kebbi ya shelanta ta cewa, zai bada tallafi ga manoman shinkafa da kuma kara musu karfin gwiwar yin noma a Jihar Kebbi musamman noman shinkafa.

Furucin hakan ya fito ne daga bakin Shugaban Kamfanin Casar Shinkafar Dakta Hussaini Suleiman Kangiwa.
Shugaban Kamfanin Casar Shinkafar Dakta Hussaini Kangiwa ya ya sanar da hakan ne a lokacin ya kai ziyarar duba ayyukan da injiniyoyi daga wani kamfanin kasar China za su gudanar a wurin gina kamfanin nasa.
Shugaban Kamfanin Casar Shinkafar yaci gaba da cewa, za mu .bada tallafi ga manoman shinkafa, mu kara musu karfin gwiwar yin noma a Jihar Kebbi musamman noman shinkafa.
Shugaban Kamfanin Casar Shinkafar ya kara da cewa, tallafin zai kunshi samar musu da taki da irin shinkafa da kuma sauran kayan gudanar da aikin gona da idan sun kammala noman sai kamfani ya saye shinkafar da suka noma kamar yadda ake sayar da ita a kasuwa.
Shugaban Kamfanin Casar Shinkafar ya kara da cewa, za su kara tallafa wa manoman tare da ba su horo na zamani kan aikin noman shinkafa na zamani don kara inganta noman shinkafa a sauran kananan hukumomin jihar.
Shugaban Kamfanin Casar Shinkafar ya kuma sanar da cewa, kara kamfanin zai kuma samar da ayyukan yi ga mutane dari biyar.
A cewar Shugaban Kamfanin Casar Shinkafar, kimanin mutum dubu biyar ne za su samu aiki a kamfanin da yake ginawa a karamar Hukumar Argungu da ke Jihar Kebbi.
A cewar Shugaban Kamfanin Casar Shinkafar, ma’aikata 1,500 ne za su kasance ma’aikata na dindindin, sauran 3,500 za su kasance ma’aikatan wucin gadi da na kwantaragi da kuma wadanda za ana biya a kullum.
Shugaban Kamfanin Casar Shinkafar ya cigaba da cewa, ya yi tunanin kafa kamfanin casar shinkafa a garin Argungu ne don samar da ayyukan yi ga jama’armu da kuma taimaka wa gwamnatin jihar da kuma ta tarayya wurin samar da aikin yi ga jama’ar kasar nan; musamman matasa da ke zaman kashe wando.
A karashe, Shugaban Kamfanin Casar Shinkafa ya sanar da cewa, nan bada jimawa ba za mu kafa kamfanin samar da takin zamani a garin Kangiwa da ke karamar Hukumar Arewa don samar da saukin samun taki ga manoman Jihar Kebbi, kuma nan da wata tara masu zuwa za a yi hakan.
A wata sabuwa kuwa, kungiyar Manoman Shinkafa ta kasa reshen jihar Lagos (AFAN) ta sanar da cewa, ta samu filin noma mai kadada 200 a jihar don yin noman Shinkafa a yankin Epe
Shugabanta Mista Femi Oke ne ya sanar da hakan a hirarsa da kamfanin dillancin labarai na kasa a jihar, inda ya ce, manufar ita ce itama kungiyar ta shiga cikin fannin na noman Shinkafar da kuma kara samar da ayyukan yi a jihar.
Shugaban Mista Femi Oke ya yi nuni da cewa, Gwamnatin Tarayya ta samar da damarmaki masu dimbin yawa, mussmman kan ci gaba da ake yi, inda garkame iyakokin kasar nan da gwamnatin a mwatannin baya ta bayar da umarnin ayi don dakile shigo da kaya ta hanyar fasakauri.
A cewar Shugaban Mista Femi Oke, kungiyar ta samu gilinnne a karkashin yarjejeniyar jingina ta tsawon shekaru biyar, inda Shugaban Mista Femi Oke ya kara da cewa, kungiyar reshen jihar ta yi shiga fannin na noman Shinkafar ce don ta bayar da nata gudunmawar wajen samar da wadataccen abinci, kasa baki daya ta hanyar samar da tan-tan na Shinkafar da zata samar duk shekara.
Shugaban Mista Femi Oke ya ci gaba da cewa, munyi amanna cewar, zamu noma tamu Shinkafar a wannan kakar noman Shinkafar mai zuwa.
Shugaban Mista Femi Oke ya sanar da cewa, mun kuma baiwa yayan kungiyar mu kwarin gwaiwar dasu noma Shinkafar koda yar kadan ce yadda muma zamu bayar da gudunwa wajen kara yawan tan-tan na Shinkafar da ake bukata a kasar nan.
Shugaban Mista Femi Oke ya kuma bayyana cewa, akwai mutane da dama da suke son su rungumi yin noman Shinkafar a yankin na Epe, inda Shugaban Mista Femi Oke ya kuma yi nuni da cewa, hakan zai taimaka matuka wajen kara wada kasar nan da abinci mai dimbin yawk wanda har za a gitar dashi zuwa wasu kasashen duniya don siyarwa.
Shugaban Mista Femi Oke ya bayyana cewa, yayan kungiyar suna noma ko wanne irin amfanin gona, inda ya buga misali da cewa, yayan kungiyar ta AFAN suna yin sana’ar kiwo, noma kayan lambu, kiwon Aladu, noman Shinkafa da kuma sauran fannonin aikin noma.
Shugaban ta Mista Femi Oke ya kuma yi kira ga Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohin dake kasar nna dasu taimakawa manoman na Shinkafa da kayan aiki na zamani yadda zasu samu damar noma Shinkafar mai yawa a kasar nan wadda zata iya wadar kasar nan da kuma fitar da ita zuwa kasashen waje.
A cewar Shugabanta Mista Femi Oke, manoman kasar nan, musamman wadanda suke a karkara suna fuskantar matsalar rashin kyawawan hanyoyi, inda hakan yake zamar masu babbar matsala wajen safaffar amfanin gonar da suka noma zuwa gidanjen da kuma kasuwanni.
Shugaban Mista Femi Oke ya sanar akwai bukatar gwamnatin data bude hanyoyin dake a karkara, wadanda kuma suke hada kauye da kauye, kamar yadda kungiyar ta yi a kadada 200 da kungiyar ta samar a garin Epe.

Exit mobile version