Connect with us

NOMA

Dalilin Wasu Manoman Zamfara Na Maida Hankali Kan Sabon Irin Sorghum

Published

on

Manoman Sorghum da ke cikin jihar Zamfara sun bayyana cewa sun rungumi yin amfani da sabon ingantattacen irin sorghum seeds da ake kira da CSR-01 saboda yadda ake samunb ambarka mai dimbin yawan gaske idan aka kwatatnta da sauran irin da aka sani.

Manoman sun sanar da hakan ne a taron shekara-shekara na 2019 na noman rani da makarantar FFBS da IFAD suka shirya a jihar Zamfara.

Sabon irin na CSR-10 sorghum an gabatarwar da Manoman ne ta hanyar IFAD da kuma CASP.

Har ila yau, Manoman sun shedawa jaridar Daily Trust hakan ne yankin Kwaren Ganuwa da ke a cikin karamar hukumar Tsafe da ke a cikin jihar ta Zamfara, inda suka yi nuni da cewa, sabon irin na Sorghum CSR-01 zai samar masu da girbin day a kai daga kwanuka 80 zuwa kwanuka 86 na shuka shi, sabanin irin na gargajiya day a kaiwa kwanuka 100 bayan an shuka shi.

Wani Manomi a jihar Tukur Muhammad ya sanar da cewa, lokacin da yazo dashi ya kuma shuka shi, mafi yawancin manoma takwarorin sa sun dauka cewar ba zai yi wani aiki ba domin suna gani kamar anyi a ne a makare, inda ya kara da cewa, amma kuma gashi amfanin ya girma kuma ana shirin a girbe shi a cikin kwanuka 86.

Tukur Muhammad ya cigaba da cewa, dubban Manoman daga baya sun nuna suna da ra’ayin sa saboda yadda ya ke samar da amfanin gona mai yawan gaske.

Shi ma wani Manomin mai suna Aliyu Yusha’u ya bayyana cewa duk da bai taba yin amfani da sabon irin ba, amma wani abokinsa ya sheda masa cewa, irin yana da alfanu sosai.

Bugu da kari, Manoman sun kuma koka akan irin Ciyawar da ake kira Strigar da akafi sani da kuduji, inda hakan ya sanya ba’a samun wani amfani gona mai yawa.

Ya sanar da cewa, Ciyawar ta strigar tana mamaye jijiyoyin amfanin da aka shuka tare da shanye ruwa da tsotse takin zamani, inda hakan ya ke sanya amfanin da aka shuka matsalar rayuwa.

Sai dai, wani jami’I a IFAD-CASP ya shedawa jaridar Daily Trust ta ranar Lahadi cewa, Ciyawar ta strigar za’a iya maganin ta hanyar yin amfani da gargajiya da ake kira sassarya da Manoma su ke zubawa bayan a lokacin yin girbi.

A nasa bangaren wani jami’in shirin IFAD-CASP da ke a jihar Zamfara Dakta Tukur Muhammad ya sanar da cewa, Manoman da ke a karkara, suna fuskantar matsalar numamar yanayi, musaman a Arewacin kasar nan.

A cewar Dakta Tukur Muhammad ya kara da cewa, matsalar numamar yanayi, tana kara zamowa Manoman da ke a karkara barazana, inda ya kara da cewa, an kuma koyawa Mnaoman dabarun da zasu kara habaka amfanin sun a gona.

Advertisement

labarai