Dalilina Na Neman Wakilcin Kananan Hukumomin Kura, Madobi Da Garun Malam A Majalisar Tarayyar Nijeriya -Hon. Sarki

 

Tsarin mulkin dimokaradiyya ya yi tanadi na samar da wakilci al’umma a matakai daban daban domin isar da buƙatun al’umma da gudanar da mulkin da yawunsu. A bisa wannan tsarin Kananan Hukumomin Kura, Madobi da Garun Malam sun kasance karkashin wakilai daban daban na tsawon shekaru 22 tun bayan dawowa mulkin dimokaradiyya a shekara ta 1999.

Wannan wakilci abu ne mai matuƙar muhimmanci da alfanu ga al’umma ta hanyoyi da dama. Daga cikin alfanun wannan wakilci akwai gina al’umma ta hanyar tallafa musu wajen samun ilimi, koyarwa tare da bada tallafin sana’o’i ga mata da matasa, samar da ayyukan yi ga tarin matasa da suka kammala karatu, samar da magunguna a asibitici domin al’umma, gyara da gina sabbin hanyoyi a yankunan karkara, tallafawa manoma da yan kasuwa domin inganta sana’o’insu da dai sauransu kasancewar akwai tanadi da Gwamnati ta yi na baiwa wakilan kudade don aiwatar da wadannan ayyuka. Abin mamaki shi ne yadda muka gaza amfanuwa da irin wannan tanadi domin a iya tsawon wannan lokacin wadannan yankuna namu na fama da ƙalubalai na rashin samun wadannan abubuwa dana lissafa dai dai da kason da aka baiwa wakilan namu a tsawon shekaru 22 da suka gabata.

Allah ya azurta Kananan Hukumomin Kura, Madobi da Garun da kasar noma da kuma ruwa da ake noman rani dashi kuma al’ummarmu sun duƙufa wajen noma na rani da damuna sannan sunyi fice wajen noma shinkafa mai yawa da ake fitarwa zuwa yankuna daban daban na kasar nan harma da kasashen waje da kuma kayan rafi amma a tsawon shekaru 22 ana wannan wakilci babu wani kuduri da wakilanmu suka gabatar don neman Gwamnati samar da kamfanoni na sarrafa shinkafa da kayan rafi da ake nomawa a wadannan yankuna musamman karamar hukumar Kura. Bayan haka Allah ya azurta Kananan Hukumomin Kura, Madobi da Garun Malam da tarin matasa da suka kammala karatu a makarantu daban daban suna nan zaune babu aikin yi amma a tsawon shekaru 22 babu wani wakili da a lokacinsa ya iya samawa matasa da yawansu yakai 15 aiki.

Haka zalika babu wani wakili da gina matasa ko mata ta fannin sana’o’i da a yau zaiyi alfahari dasu. Idan muka duba maganar hanyoyi abin akwai takaici domin yankunanmu na fama da matsalar hanyoyi musamman babbar hanyar data tashi daga sabon titin Panshekara zuwa Madobi wacce ta Gwamnatin Tarayya ce amma tsawon shekaru 22 ta lalace amma babu wani wakili daya taba miƙa kokon bararmu a gaban Majalisar Tarayya, akwai gada data hada Kananan Hukumomin Kura, Madobi da Garun Malam wacce Gwamnatin Malam Ibrahim Shekarau ta yi wacce ta karye tana buƙatar gyara amma babu wani yunƙuri na samar da gyaran tare da karasa titin.

Sannan akwai hanyoyi da dama a wadannan yankuna da suke buƙatar gyara amma babu wani kokari wajen aiwatarwa. A yau asibitocinmu na fama da rashin kayan aiki da magunguna wanda wakilan zasu iya samawa daga cikin kudaden Constituency Projects amma duk hakan bata samu ba. Idan ka dauki maganar ruwan sha, har yanzu wannan matsala tana addabar al’umma a yankuna da dama na wadannan Kananan Hukumomi wanda itama za’a iya tunkararta ta hanyar constituency projects domin wadannan abubuwa sune buƙatar al’umma kuma sune abubuwan da al’umma za ta iya amfana dasu kai tsaye daga wakilanmu.

A bisa wannan ƙalubalai ne naga dacewar fitowa domin neman wakilcin wadannan yankuna namu domin kawo sabon tsarin wakilcin da zai bada fifiko ga dukkan buƙatun al’umma kamar yadda na bayyana. Burina shi ne gina wani tsarin wakilci da zai samar da wani dandalin tattaunawa da al’umma a matakin kowacce karamar hukuma lokaci zuwa lokaci don sanin buƙatun al’umma tare da karbar shawarwari don kyautata wakilcin da muke fatan gudanarwa idan Allah SWT ya amince mana.

A wannan gaba nake kira ga al’ummarmu na Kura, Madobi da Garun Malam musamman matasa da su dubi wannan ƙudurori namu kuma su bamu goyon baya don tabbatuwarsu. A karshe ina adduar Allah SWT ya cigaba da yi mana jagoranci kuma ya azurta wadannan Kananan Hukumomin namu da samun kyakkyawan wakilci da shugabanci a kowanne mataki.

Exit mobile version