Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home SIYASA

Dalilina Na Sake Tsayawa Takarar Shugabancin Ƙungiyar Marubuta Ta Ƙasa –Denja

by Tayo Adelaja
October 3, 2017
in SIYASA
5 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Ƙungiyar Marubuta ta Ƙasa (ANA) ta na a ƙarƙashin jagorancin Malam Denja Abdullahi daga 2015 zuwa yau, ya kuma kafa tarihin kyakkyawan shugabanci a ƙungiyar a matsayin jajirtaccen haziƙin shugaban da ya jagoranci ingantattun manufofi da sauye- sauye masu amfani da alfanu a duniyan rubutu da marubuta.

Daga, Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto

A yanzu haka manbobin ƙungiyar ANA sun shirya tsaf domin gudanar da zaɓen ƙungiyar wanda za a gudanar a babban taron ƙungiyar na ƙasa karo na 36 a Birnin Makurdi na Jihar Benue a ranakun 26 zuwa 29 ga Oktoba.

Shugaban Ƙungiyar Denja Abdullahi ya bayyana cewar a shugabancin da ya gudanar na tsayin shekaru biyu ya taka muhimmiyar rawar ciyar da ƙungiyar a gaba, don haka ya cancanta ya sake neman shugabanci a karo na biyu.

Denja ya ce” A tsayin shekaru biyu na gudanar da ingantaccen mulki na kuma samu nasarori da dama waɗanda a bayyane suke mun kuma wallafa a cikin kudin bayanan nasarorin mu don haka mene ne dalilin da zai sa in kasa tsayawa takara a karo na biyu? Ya tambaya.

A cewar sa “Mafi yawan manbobin ƙungiyar waɗanda suka bayyana mani ra’ayoyinsu da cewar matakin da aka ɗauka shine in sake tsayawa takara a karo na biyu domin in ƙarasa muhimman ayyukan da na assasa. Ƙalubale yana a gaban waɗanda ke ganin ban cancanta ba, sai su bayyanawa babban taro dalilin rashin cancanta ta?” Inji shi.

Shugaban ya bayyana cewar manbobin ANA na ƙwarai suna da masaniyar abin da ya fi cancanta ga ƙungiyar a kowane irin lokaci kuma su ne waɗanda za su tabbatar da zaɓensa ko akasin sa. “Ina da tabbacin irin kyakkyawan shugabanci da na gudanar ina kuma da yaƙinin za a sake zaɓe na a karo na biyu kuma na ƙarshe.” Ya bayyana.

Shugaban Ƙungiyar ya kuma bayyana cewar kasancewar wannan shekarar ta zaɓe ce, marubuta da ke zama ba su zuwa taro sai shekarar zaɓe kawai su canja tunani su yi abin da ya kamata. “Abin da ya kamata shine su biya kuɗaɗen ƙungiya na shekarar da ta gabata idan har ba su yi rajista a babban taron waccan shakarar ba tare da biyan kuɗin rajista na wannan shekarar, Idan suka yi haka sun zama cikakkun ‘ya’yan ƙungiya da za su iya gudanar da zaɓe.”

Denja ya ce sun san waɗanda suka cancanta da zama halastattun ‘ya’yan ƙungiya domin suna da kundin bayanai domin tantancewa. A kan sababbin manbobi kuwa ya ce suna yi masu maraba amma kuma akwai iyakar da ba za su iya wucewa ba a taron ƙungiyar wanda ba na zaɓe ba ballantana kuma taron zaɓe.

A ƙarƙashin jagorancin Denja ƙungiyar ta samu nasarori da daman gaske har guda 35 daga ciki akwai; Ƙaddamar da muhimman kwamitoci a taron farko a ranar 9 ga Janairu 2015 domin tabbatar da cika manufofin ƙungiya. Kwamitocin da aka ƙaddamar sune, babban kwamitin bayar da shawara na ƙasa kuma irinsa na farko wanda ya ƙunshi uku daga cikin tsofaffin shugabannin ƙungiyar na ƙasa da uku daga cikin dattawan ƙungiya, da kuma samar da Muhimmin Kundin Ayyukan ANA, wanda aka tsara dukkanin abubuwan da ƙungiyar za ta gudanar na tsayin shekaru biyar 2017-20122, abu na uku kuma shine ƙaddamar da kwamitin kula da gina filin ANA sai kuma kwamitin alƙalai waɗanda za su kula da gasar ANA.

A yanzu haka a ƙarƙashin jagorancin Denja Abdullahi, an fara ginin Sakatariyar Ƙungiyar ta Ƙasa a filin da ƙungiyar ta gada shekara da shekaru a Mpape Abuja.

Ƙungiyar ANA ta shige kan gaba wajen yaƙin neman a sako manbanta da ke ɗaure a Kurkuku kan laifin ɓatanci a wani littafi da ya rubuta tare da wani basarake a Bayelsa. Nenghi Josef Ilagha wanda aka ɗaure a Nuwamba 2015 an sake shi a ranar 26 ga Afrilu 2016 bayan matsin lamba daga ƙungiyar.

Ƙungiyar Marubuta ta Nijeriya ta shiga cikin aikin sake bitar dokar hakkin mallaka ta hanyar gabatar da ingantattun bayanai kan tsarin da aka gabatar mata daga Hukumar Kula da Hakkin Mallaka ta Ƙasa wanda kuma hukumar ta yabawa ƙwazon ANA kan gudummuwar da ta bayar.

A ranar 3 ga Yuni 2016, ANA ta ƙulla yarjejeniya da fitaccen kamfani Boɗ Office Studios Ltd a Abuja kan shirya shirin musamman na kallo da na sauti kan tarihin ANA, ayyukan ta da nasarorin ta. An kammala shirin a Disamba 2016 an kuma nuna shirin mai taken “Dancing Mask: The ANA Story’ a dadalin nuna fina-finai na Abuja a Fabrairu 2017. An gudanar da shirin ne da tallafin kuɗi daga ƙungiyar Pan African Writers Association (PAWA)

Shugaban Ƙungiyar ANA ya sanya manbobin da za su yi alƙalanci a ƙarƙashin jagorancin Tsohon Shugaban ANA kuma manba na kwamitin bayar da shawara na ƙasa Dakta Wale Okediran domin magance matsalar rikicin shugabanci na tsawon shekaru huɗu a reshen ƙungiyar da ke Jihar Neja. Tawagar ta ziyarci Jihar Neja a ranar 4 ga Satumba 2016, an kuma samu gagarumar nasarar shawo kan matsalar an kuma naɗa kwamitin riƙon ƙwarya.

Ƙungiyar ANA a karon farko ta gudanar da taron ƙarawa juna sani na ƙasa kan ƙananan marubuta masu tasowa daga 27 zuwa 30 ga Satumba 2016, taron ya karɓi baƙuncin makarantu mahalarta 20 a ciki da wajen Owerri, jihar Imo, an kuma horas da ƙananan yara 15 daga rassan jihohi 15 a faɗin ƙasar nan.

Bugu da ƙari ANA ta samu nasarar gudanar da karɓaɓɓen babban taro na ƙasa karo na 35 a Abuja daga 27 zuwa 30 ga Oktoba 2016 wanda Sanata Shehu Sani ya baƙunta tare da samun halartar uwargidan Gwamnan Jihar Imo, Misis Nnena Rochas Okorocha da sauran muhimman mutane.

A karo na farko a tarihin Ƙungiyar Marubuta ta Ƙasa, baya ga babban taron ƙasa da aka gudanar a Abuja a 1985, an zagaya da manbobin ANA waɗanda suka halarci babban taro na 35 a filin ƙungiyar da ke Mpape, Abuja.

Shugabannin ƙungiyar ANA, waɗanda suka himmatu wajen ƙarfafa tafiya kan tsarin zaɓe a dukkanin rassan ƙungiyar a faɗin ƙasa sun bayar da goyon baya da sanya idanu kan zaɓukan ƙungiyar a rassa da ke a Akwai- Ibom, Benue, Abuja, Nasarawa, Kaduna, Ribas, Kwara, Kogi, Osun, Ekiti, Kano, Zamfara, Abia, Bayelsa da kuma Kebbi a cikin shekarar da ake ciki.

Denja Abdullahi wanda Darakta ne a Cibiyar Fasaha da Al’adu ta Nijeriya ya fara bayar da gudunmuwa a ƙungiyar marubuta ta ƙasa a farkon shekarun 90’s, kuma shine ya jagoranci kafa ANA a jihar Kebbi a wancan lokacin.

Shugaban ya riƙe mabambantan muƙamai a ƙungiyar daga ciki akwai Mataimakin Sakatare na Ƙasa a taron Makurdi 2003, daga nan likkafa ta yi gaba aka zaɓe shi a matsayin Sakataren Ƙungiyar na Ƙasa a taron Kano a 2005, an kuma sake zaɓen sa ba tare da hamayya ba a taron Owerri 2007 a matsayin Babban Sakatare. Daga 2011 zuwa 2015 Denja Abdullahi ya kasance Mataimakin Shugaban ANA, daga nan kuma ɗimbin haziƙƙan marubuta suka jefa masa ƙuri’ar zama Shugaban Ƙungiyar na ƙasa bakiɗaya bisa ga himma, ƙwazo da jajircewa wajen ciyar da ƙungiyar a gaba lamarin da a yau bayan shekara biyu saman kujerar, marubuta maza da mata suka sake bayyana shi a matsayin wanda suke muradin ya ci-gaba da jagorancin ƙungiyar a karo na biyu bayan gamsuwa da shugabancin sa.

SendShareTweetShare
Previous Post

Jam’iyyar APC Ta Yiwa PDP Tumɓur a Zaɓen Maye Gurbi A Legas

Next Post

Duk Runtsi Ba Zan Bar PDP Ba –Sule Lamiɗo

RelatedPosts

Jiga-jigan Jam’iyyar PDP Sun Ziyarci Goodluck Jonathan

Jiga-jigan Jam’iyyar PDP Sun Ziyarci Goodluck Jonathan

by Muhammad
2 weeks ago
0

Kwamitin sulhu na musamman na Jam'iyyar PDP, karkashin jagorancin tsohon...

Har Yanzu Sakkwatawa Ba Su Fara Morar Dimukradiyya Karkashin Mulkin Tambuwal Ba – Umar Lili

Har Yanzu Sakkwatawa Ba Su Fara Morar Dimukradiyya Karkashin Mulkin Tambuwal Ba – Umar Lili

by Nasir Gwangwazo
6 months ago
0

Shugaban kungiyar matasan jihar Sokoto kuma dan gwagwarmayar ganin an...

Wane Ne Hon. Mal Samaila Suleiman (Dujiman Zazzau)?

Wane Ne Hon. Mal Samaila Suleiman (Dujiman Zazzau)?

by Daurawa Daurawa
8 months ago
0

Hon. Malam Sama'ila Sulaiman (Dujiman Zazzau) an haifeshi ranar 03/02/1981,...

Next Post

Duk Runtsi Ba Zan Bar PDP Ba –Sule Lamiɗo

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version