Dalilinmu Na Kin Bayyana Jami’an Da Aka Tura Lekki Tolget Ba – Sojoji

Daga Rabiu Ali Indabawa

Sojojin Nijeriya sun bayyana cewa ba za su bayyana sunayen mutanensu da aka tura zuwa Lekki tollgate a ranar 20 ga Oktoba, 2020 ba. Idan za ku tunawa cewa sojoji sun tarwatsa masu zanga-zangar #EndSARS, wadanda suka hana zirga-zirgar ababen hawa a wannan hanya tsawon makonni biyu.

Wannan mummunan lamarin ya haifar da martani daban-daban a ciki da wajen kasar kamar yadda ake zargin sojoji da gwamnatin tarayya da cin zarafin bil adama.

Ko da yake rahotanni da dama sun nuna cewa sojoji da yawa sun kashe mutane da yawa amma akwai bukatar tabbatar da wannan lamarin har yanzu. Kakakin runduna ta 81 na rundunar sojojin Nijeriya, Osoba Olaniyi a wata hira da jaridar PUNCH ya ce ba ya daga cikin kwarewar aikin rundunar idan har ta sanya sunayen sojojin da ke aiki a ranar.

“Ya sabawa aikin tsaro. Hakan ba mai yiwu wa bane, ya sabawa manufar tsaro. Babu matsala a nan. Hoton da wasu mutane ke zanawa, kamar muna fada da gwamnatin jihar, ba daidai ba ne, “Kamar yadda jaridar ta nakalto shi yana cewa.

Da farko sojojin sun musanta cewa su ke da alhakin lamarin. A wasu sakonni na tuwita, rundunar ta bayyana rahotannin kan sojoji da suka bude wuta a harabar a matsayin labarai na bogi. Amma a makon da ya gabata, Olaniyi ya tabbatar da cewa sojoji ne suka aiwatar da aikin.

Olaniyi a baya ya bayyana cewa gwamnatin Legas ta gayyaci sojoji don dawo da zaman lafiya bayan rikice-rikice da yawa. “Babu wani lokaci da sojojin  Nijeriya suka bude wuta kan kowane farar hula. Tun daga farkon zanga-zangar ta ENDSARS, babu lokacin da jami’an runduna ta 81 ta sojojin Nijeriya da ke Legas suka shiga ciki, ”in ji shi a cikin wata sanarwa.

“Duk da haka, Gwamnatin Legas (LASG) ce ta yanke shawarar kiran sojoji, bayan kafa dokar hana fita ta sa’o’i 24. “Wannan ya faru ne sakamakon tashin hankalin wanda ya kai ga kona ofisoshin‘ yan sanda da yawa, aka kashe ‘yan sanda, aka saki wadanda ake zargi a hannun ‘yan sanda da kuma makamai da suka kwashe. Yanayin ya kasance yana dada tabarbarewa cikin rikici. A wannan lokacin ne LASG ta nemi sojoji da su sa baki domin dawowa yadda aka saba.

“Shigar da sojoji suka yi ya bi duk hanyoyin da aka shimfida na ayyukan Tsaron Cikin Gida kuma duk sojojin da aka aika sun yi aiki ne a cikin tsarin Dokar Hadin Kai (ROE) irin na ayyukan Tsaron Cikin Gida.”

 

Exit mobile version