Abubakar Abba" />

Dalilinmu Na Noma Tumbar Kadada 15,000 Na Roba A Kuros Ribas – NARPPMAN

Akwai alamun dake nuna cewa, akwai fata nagari a fannin noma Roba a Nijeriya bayan da masu ruwa da tsaki a fanin suna nuna cewar a shirye suke su farfado da fannin, inda a jihar Koros Ribas, aka ware kadadar yin noma 15,000 don nomanta a jihar.

kungiyar masu sarrafa roba ta kasa (NARPPMAN) ce ta bayyana hakan, inda ta kara da cewa, an samar da shirin yin nomanta, inda aikin zai kai shekaru 10 ana gudanar da shi kuma aikin ya hada da shuka sabbin iri.
Shugaban kungiyar ta reshen jihar Koros Ribas Rabaran Umo E. Inameti ne ya sanar da hakan a lokacin day a kaddamar da kungiyar ta kananan ukumomi a cikin jihar ta Koros Ribas da aka gudanar a garin Kalaba.
A cewar Shugaban reshen jihar Koros Ribas Rabaran Umo E. Inameti, kirkiro da kungiyar ya zama wajibi idana akayi la’akri da irin dimbin mahimmancin da noman rubber yake dashi.
Shugaban kungiyar reshen jihar Koros Ribas Rabaran Umo E. Inameti ya ci gaba da cewa, a bisa la’akarin da aka yi na ganin masu ruwa da tsaki a jihar ta Koros Ribas wajen mayar da hankali kan farfado da nomanta a jihar.
Ya sanar da cewa, kamar irin yunkurin gonar Royal International, kungiyar ta NARPPMAN zata kuma tabbatar da ta kirkiro da ayyukan yi guda 90,000 na kai tsaye da kuma wadanda ban a kai tsaye ba a jihar ta Koros Ribas, tare da daukar mutane su 45,000 da kuma karin daukar matasa guda 50,000, aikin yi kai tsaye.
Shugaban kungiyar reshen jihar Koros Ribas Rabaran Umo E. Inameti Inameti ya kara da cewa, farfado da fannin na noman ta a jihar zai taimaka wa jiahr ta matuka wajen sake farfado da fannin na nomanta a jihar.
Umo E. Inameti ya kara da cewa, mu na shirin nomanta a kadadar noma kimanin 15,000 nan da shekaru 10 masu zuwa 10.
A cewar Shugaban kungiyar reshen jihar Koros Ribas Rabaran Umo E. Inameti, hakan zai taimaka matuka wajen samar da kudadens higa kimain naira biliyan 40 ko sama da hakan a duk shekara ga gawamnatin jihar ta Koros Ribas.
Shugaban kungiyar reshen jihar Koros Ribas Rabaran Umo E. Inameti, ta hakan zamu bayar da tamu gudunmawar wajen samar da ayyukan yi da kuma samar da ci gaba a jihar ta Koros Ribas.
A cewar Shugaban kungiyar reshen jihar Koros Ribas Rabaran Umo E. Inameti, fannin na noman ruber a jihar ta Koros Ribas abune da akayi watsi dashi, inda a yanzu, kungiyar take son ta sake farfado da shi.
Shugaban kungiyar reshen jihar Koros Ribas Rabaran Umo E. Inameti ya ce, manufar mu shine mu sake farfado da nomanta a jihar ta hanyar shuka Irin na ruber mai yawa a kadadar yin noma guda 15,000.
A wata sabuwa kuwa, Sakataren Manoman Jihar Kebbi Alhaji Mohammad Idris Birnin Kebbi ya ce ban-ruwa ne matsalar manoman jihar, inda ya ci gaba da cewa, wannan shiri zai taimaki manoman Kebbi har su iya ciyar da kasa da abinci.
Alhaji Mohammad Idris wanda ya sanar da hakan a wani taron masu ruwa da tsaki a fannin na noman rani ya kuma yi kira ga gwamnatin ta fadada shirin ya kai dukkan kananan hukumomi 20 na jihar kuma a shigo da sarakunan gargajiya da manoman gaskiya domin samun nasara.
Gwamnatin Tarayya ta ba da sanarwar da cewa, ta tallafa wa manonam rani dake a jihohin Zamfara da Kebbi a bisa yunkurin tan a kara inganta noman, sabanin yadda suke yin amfani da kananan rijiyoyin burtsatse a cikin sana’ar ta su.
Daraktan noman rani da magudanun ruwa a dake a ma’aikatar ruwa ta Tarayya, Mista Elijah Aderibegbe ne ya sanar da hakan, a kokacin taron na masu ruwa da tsaki a fannin, inda ya ci gaba da cewa, aiwatar da tsarin wani bangare ne na yunkurin da ake yi na karfafa noman rani a Nijeriya baki daya.
Mista Elijah Aderibegbe ya ce abu ne da zai kara habaka aikin noma da samar da wadataccen abinci ga Nijeriya.
Tsarin jigogin shida za a yi su a Jihar Kebbi, uku za a kai su Zamfara, an yi haka ne domin a zaburar da manoma kan aikin noma na zahiri a Arewa ta Yamma ganin yankin ya yi fice a harkar noma.
Ma’aikatar Ruwa ta mika jigogin ban ruwan guda tara ga Hukumar kogin rima da ke jihar Sakkwato, har iala yau, ana sa ran samar da jigogin ya kara habaka aikin noman rani da kawar da barnar ruwa a lokacin ban-ruwan noman rani.
Bugu da kari ana kuma son a dakile almubazaranci da ruwa abu ne da duniya ta sanya a gaba kuma an samar da shi ne bisa muhimmanci ga harkar noma don ba a son amfanin gona ya samu karancin ruwa.
A kwanna baya ne dai, Bankin Duniya ya fitar da kididdiga cewa aikin noma ke lashe kashi 70 ckin a cikin dari na ruwan da ke yawo a duniya, onda noman rani bai samar da abincin da ake bukata.

Exit mobile version