Connect with us

LABARAI

Dalilinmu Na Raba Magunguna Kyauta Don Masu Juna Biyu – Zainab Ghana

Published

on

A bisa cigaba da gudanar da ayyukan jin kai da ga alummar jihar Katsina, musamman alummar da ke a karkara, Shugabar kungiyar jin kan alumma  ake kira Woman for Woman Initiatibe da ke a jihar Katsina Hajiya Zainab Abdu Ghana, ta rabar da magungunan Asibiti kyauta ga wasu Asibitocin da ke a jihar, musamman don kula da lafiyar  masu juna biyu da yara kanana da ke a jihar Katsina.

Hajiya Zainab Abdu Ghana wacce kuma sananniyar yar siyasa ce a jihar Katsina, musamman a karamar hukumar ta Funtua a hirararta da Leadership Ayau ta ce, kungiyar ta rabar da irin wadannan magungunan a Asibitin da ke a garin Funtuwa cikin jihar Katsina.

Shugabar wacce tsohuwar yar takarar Kujerarar  Majalisar Dokokin jihar Katsina ce ta ce, ta rabar da magungunan ne kyauta daga cikin ayyukan da kungiyar ta saba yi na jin kan alumma da ke a fadin jihar Katsina, musamman alumar da ke a karkara a cikin jihar don ceto rayukan  masu juna biyu da kuma yara kanana da ke a yankunan da suka amfana na jihar.

Hajiya  Zainab Abdu Ghana ta cigaba da cewa, kamar a karamar hukumar Musawa da ke a cikin jihar, abinda na sani game da magungunan,  ni Shugabar wannan kungiya, da kaina  na jagoranci rabon magunguna da kungiyar ta raba, inda ta kara da cewa, kusan kowace shiya uku da mu ke da su a jihar Katsina mun zabo wasu  kananan hukumomin da ke a cikin shiyoyin uku don rabar da magungunan kyauta.

Hajiya Zainab ta sanar da cewa, kananan hukumomin da suka amfana da tallafin magungunan sun hada da Faskari, Bakori, Funtua, Danmusa, Katsina da kuma Daura.

A cewar Hajiya Zainab, Malumfashi kuma na maku alkawari duk abinda ya taso irin wannan da kaina zanzo in kawo kamar yadda kowace karamar hukumar da ke a jihar, da kaina nakai masu magani kuma ba tare da kosisin kowa ba haka nake kai magani har asibiti kyauta.

Hajiya Zainab Abdu Ghana ta kara da cewa, na bayar da magungunan ne da kyakkyawar manufa kuma Allah ya  sani.

A cewar Hajiya Zainab Abdu Ghana, da hannu na na bada maganin karamar hukumar Musawa wanda na damka amanar magani ga wasu bayin Allah su biyu, inda ta kara da cewa, a gaban Sakataran wannan kungiya Hamisu Hara da masu taimaka mana Ibrahim S Kakumi aka rabar da kayan.

Hajiya Zainab Abdu Ghana ta yi kira ga Asibitocin da suka amfana da magungunan da su yi amfani da su kamar yadda ya dace, musamman don amfanin masu juna biyu da yara kanana.

A karshe, Hajiya Zainab Abdu Ghana ta bayar da tabbacin cewa, a karkaahin wannan kungiyar da ta ke shugabanta, ba za a yi kasa a gwiwa ba, wajen gudanar da ayyukan jin kai alumma ba.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: