A ci gaba da goyon bayansa ga kananan manoma dake a kasar nan kamfanin dake sarrafa Sigari (BATNF) ya tallafa masu sana’ar sayar da Kifi dake a jihar Legas da kayan gasa Kifi na zamani kyauta.
Da ya ke jawabi a wurin mika kayan na tallafin ga yan kasuwar a lokacin taron da ya gudana a Hukumar Kula da Aikin Gona ta jihar Legas (LSADA) dake a yankin a Oko Oba a anguwar Agege Legas, Daraktan Cibiyar Uwargida Abimbola Okoya, ta bukaci masu cin gajiyar su yi amfani da kayan aiki don canza rayuwarsu.
Daraktan Cibiyar Uwargida Abimbola Okoya, ta ce, a tsawon lokaci, cikin goyon bayan da muke baiwa manoma, mun lura cewa ban da koyar da su kyawawan ayyukan gona akwai kuma bukatar samar da ingantaccen kifi kuma yana da mahimmanci a yi abubuwa uku.
A cewar Daraktan Cibiyar Uwargida Abimbola Okoya, na daya akwai koya musu hanyoyin samun ingantaccen Kidi da fitar dashi da samar masu da kasuwa da kara karfafa musu gwiwa don kara darajar sana’ar tasu.
Daraktar Cibiyar Uwargida Abimbola Okoya, ta sanarda cewa, wannan tallafni da horarwa kan kyawawan ayyuka a cikin kifin da sarrafawa da kuma shirya su, muna fatan kasuwancinku da kudin shiga mai ya wa a karshe zaku fara fitarwa zuwa kasashe na ciki da wajen yankin Afirka.
A wata sabuwa kuwa, Kwamishinan ma’aikatar gandun daji na jihar Ogun Mista Kolawole Lawal ya sanar da cewa, za’a fara aikin noman gandun daji da farfado da kawata daji a jihar.
Ya sanar da hakan ne ga manema labarai hakan a garin Abeokuta, inda ya ce, manufar aikin, ita ce don a samar da ayyukan yi musamman a tsakanin dimbin matasan dake jihar.
Idan za a iya tunawa a kwanan baya, Kwamishinan ma’aikatar gandun daji na jihar Mista Kolawole Lawal, a ofis dinsa ya gudanar da tattaunawa a da wanda ke lura da shirin Mista Pierre Decroid.
A cewar Kwamishinan na ma’aikatar gandun daji na jihar Mista Kolawole Lawal, gwamnatin jihar za ta kuma wayar da kan alumomin da ke zaune a yankunan da za a gudanar da aikin, musamman gannin alfanun da aikin yake dashi ga raywar su, ya kara da cewa, aikin zai amfani alumomin da ke yankin da zama ganin cewar ta hanyar aikin za su samu dimbin ayyukan yi harda dimbin matasan da ke zaune a yankuna, inda ya kara da cewa, baya ga hakan, aikin zai taimaka matuka wajen yakar dumamar yanayi da kuma kara samar da abinci mai yawa a jihar.
Kamfanin dillancin labarai na kasa a kwanan baya ya ruwaito Gwamnan jihar ta Ogun Ibikunle Amosun ya jagoranci wata tawagar kula da dumamar yanayi data zo jihar daga Majalisar Dinkin Duniya, inda kuma tawagar, ta yi amfani da damar zuwa jihar, inda tawagar ta tattauna da jami’an kamfanin Lafarge Holcim da sauran masu zuba jari kan aikin farfado da kawata gandun.
Decroid ya jinjina wa gwamnatin jihar kan samar da wannan shirin, inda ya yi nuni da cewa, aikin zai zamo abin alfahari ga kowa, indan an kammala shi.