A cikin makon nan nan ne gwamnatin jijhar Kaduna, ta hannun Kwamishinan ma’aikatar kula da Kananan Hukumomi ta bayar da wata takardar tuhuma ga masu zaben Sabon Sarkin Zazzau su hudu, inda bayyana cewa ana tuhumarsu ne bisa laifin kin halartar zaman da gwamnatin ta kira a shirye-shiryen baiwa sabon Sarkin sanda.
Takardar tuhumar mai dauke da lambar MLG/CA/36/BOL.BI/1059, tana dauke ne da sa hannun Babban Sakataren ma’aikatar, Musa Adamu a madadin Kwamishinan, Alhaji Jafaru Sani, inda a ciki aka bayyana cewa ana tuhumarsu ne a matsayinsu na ’yan majalisar Masarautar Zazzau, amma ba don suna masu zaben Sarki ba.
Wadanda aka ba wannan tuhuma, sun hada da Wazirin Zazzau, Alhaji Ibrahim Aminu; Limamin Kona, Alhaji Sani Aliyu; Limamin Zazau, Alhaji Dalhat Kasimu da Makaman Zazau Karami, Alhaji Mahmoud Abbas.
Sai da kuma akwai raderadi da ke yawo, wanda gwamnati ba ta ce komai a kai ba, cewa yanzu haka gwamnatin ta dakatar da Wazirin Zazzau, Alhaji Ibrahim Aminu daga mukaminsa, wanda kuma wannan dakatarwa ta fara aiki ne nan take.
Takardar tabbatar da dakatarwar da aka ba Wazirin, wacce majiyar mu ta tabbatar wa da wakilinmu, Babban Sakatare na ma’aikatar kula da Kananan Hukumomi da masarautu ta jihar, Alhaji Musa Adamu ne ya sanya wa hannu a madadin Kwamishinan Hukumar, Alhaji Jafaru Sani, kuma tuni takardar ta kai ga hannun wazirin Zazzau.
Binciken da wakilin LEADERSHIP A Yau ya yi kan wannan dambarwar ya gano cewar, zargin da ake yi wa Wazirin Zazzau da ta kai ga gwamnatin jihar Kaduna ta ta bayar da umurnin dakatar da shi, shi ne, a lokacin da gwamnatin jihar ta bayyana tsayar da ranar Litinin 9 ga watan Nuwambar shekara ta 2020 ta zama ranar da Gwamnan jihar Kaduna zai mika sandar Sarautar Zazzau ga sabon Sarkin, an gudanar da tarurruka a fadar Zazzau da wakilan gwamnatin jihar, a matsayin Wazirin Zazzau na kasancewa babban dan Majalisar Masarautar, an aika masa da takardar bukatar halartar wannan taro, amma bai kasance a wajen taron ba, ko da sau daya.
Binciken da wakilinmu ya yi, ya ji a majiya mai karfi cewar, Wazirin Zazzau ya amsa wannan takarda ta tuhuma da ake yi masa, inda ya ce bai samu damar zuwa ba ne a dalilin batun zaben Sarkin da gwamnatin jihar Kaduna ta yi yana gaban kotu, shi ya sa ya nemi shawarar Lauyansa, sai Lauyansa ya ba shi shawarar kada ya halarci wannan taro.
Wannan amsa da Wazirin ya bayar na tuhumar da ake yi masa, sai kuma aka ba shi takardar dakatarwa daga matsayin Wazirin Zazzau, kuma babban dan majalisar masarautar Zazzau.
Shi dai Wazirin Zazzau, Alhaji Ibrahim Aminu, shi ne ya jagoranci zaben sabon Sarkin Zazzau da ya gudana bayan rasuwar Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris. Sauran wadanda ke cikin taragon zaben sabon Sarkin, akwai Fagachin Zazzau, Alhaji Ummaru Mohammed da Makama Karami na Zazzau, Alhaji Mohammed Abbs da Limamin Zazzau, Alhaji Dalhat Kasim Imam da kuma Limamin Kona na Zazzau, Alhaji Muhammadu Sani.
Sannan kuma idan ba a manta ba, wannan sakamakon nadin da gwamnatin jihar Kaduna ta yi wa Jakada Ahmed Nuhu Bamalli a matsayin sabon Sarkin Zazzau na 19, ya sa Iyan Zazzau, Alhaji Bashari Aminu ya kai kara babbar kotun jihar Kaduna, ya cusa gwamnatin jihar Kaduna da masu zaben Sarkin da Kwamishinan Kananan Hukumomi na jihar Kaduna a cikin karar da ke kotun da ke da zama a Dogarawa.
Amma daga bisani kotun ta yanke hukuncin cewa a ba sabon Sarki, Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli sanda, kuma gwamnatin jihar Kaduna na da ikon rantsar da shi, domin in aka ce za a bi bukatar Iya Aminu ne, zai zama babu Sarki ke nan. Amma za a ci gaba da sauraren shari’ar.
Zuwa hada wannan rahoto, karar da Iyan Zazzau ya shigar da aka ci gaba da saurara a ranar Larabar da ta gabata 18 ga watan Nuwambar wannan shekara, an sake dage sauraron karar zuwa ranar 11 ga watan Disambar wannan shekara ta 2020.
Sai dai an tsegunta wa wakilin namu cewa, akwai yiwuwar ba za a ci gaba da sauraron wannan shari’ar a wannan kotu ba, saboda wasu matsaloli da ake ganin za su iya kunno kai, da suka shafi tsaro, da kuma Lauyoyin da suke kare masu zaben Sarkin da suke wakiltarsu a wannan kotu da Mai Shari’a Kabiru Dabo ke shugabanta.