Dalilinmu Na Yi Wa Mata Masu Juna Biyu Aiki Kyauta A Tsafe –Hon. Aliyu

HON.ALIYU ABUBAKAR, Shi ne Shugaban Karamar hukumar Tsafe dake cikin jihar Zamfara. Wanda ya yi Shugabanci zango biyu a tarihin Karamar hukumar, ya bayyana nasarar da ya samu na yin muhimman ayyuka da suka hada da kokarin Cibiyar tallafawa mata masu juna biyu da Kananan yara, da kuma marasa galihu, da yadda ya samar da tituna a fadin karamar hukumar ga yadda hirarsu da wakilinmu HUSSAINI BABA ta kasance kamar haka.

Za mu so ka bayyana wa masu karatu kanka ?

Sunana Aliyu Abubakar tsafe, an haifeni a shekara ta 1973 ,a Karamar hukumar Tsafe,cikin jihar Zamfara. Na yi karatun addini a gidanmu, kuma na yi karatun Firamare a Tsafe, sannan na wuce Sakandire a Sokoto, daga nan na wuce  Kwalejin kimiyya da fasaha ta gwamnatin tarayya da ke Kauran namoda in da na yi karatun Difiloma akan sashen kudi, sai kuma nawuce Kwalejin kimiyya da fasaha ta Kano inda na yi babbar Difiloma, daga nan na yi HND, Kwalejin Kimiyya da fasaha da ke Zariya, sai kuma na wuce jami’ar Kaduna inda na yi PGD kan mulki.

 

Shin ko ka taba wani aiki kafin zamowar ka Shugaban karamar hukuma?

Eh, na yi aiki a Karamar hukumar Tsafe, na takaittacen lokaci, sannan na koma hukumar zabe mai zaman kanta ta Kasa, da ke Abuja inda na yi aikin a Jihar Kogi, daga na mayar da ni jihar Kebbi, sannan aka dawo dani gida jihar Zamfara, a nan ne na je aiki na shiga harkokin siyasa.

Shigar ka siyasa wane mukamin ka fara rike wa?

A lokacin Shugaban Kasa marigayi ‘yar aduwa, ya nada ni wakili a majalisar gudanarwa ta asibitin koyarwa na Aminu Kano, inda na yi aiki na shekara hudu. A shekara ta 2012, Allah ya ba mu iko muka ci zabe muka kafa mulki a Zamfara, a wannan shekarar na fito takarar shugabancin Karamar hukumar Tsafe, kuma Allah ya ba ni nasara na zama Shugaban karamar hukumar. Sai kuma a shekara ta 2015,na sake tsayawa takara kuma na samu nasar lashe zabe, kuma gashi ina akai yanzu muna yi wa Allah godiya akan wannan baiwar da Allah ya yi mana, a tarihin Karamar hukumar Tsafe ni ne wanda ya taba yin shugabancinta sau biyu .

 

Kai ne na farko da ka taba shugaban wannan karamar hukuma har sau biyu, mene ne siriin abin?

Ina yi wa Allah godiya a kan nasarorin da muka samu, domin ba dabara ta ko iko na ba ne, a’a wannan hikima ce ta Allah da baiwarsa da ya yi mani. Kuma ‘yan ayyukan da na yi a Karamar hukumar ne ya sa na koma a karo na biyu. kuma Karamar hukuma a yanzu bakamar irin ta da ba ce, amma muna alfahari da nasarorin da Allah ya ba mu, domin ba iyawar mu ba ce yin Allah ne, mu ka yi gwargwadon halin mu, kuma muka yi gwargwadon yin mu da kudin da su ka shigo hannun mu, don amana ce aka ba mu, kuma muna kokarin sarrafa masu da amanar inda ya dace.

 

A shekara biyar da ka yi kana mulki wane kokari majalisarka ta yi wajen bunkasa harkar lafiya a karamar hukumar?

A shekara ta 2012, wajen kamfen dina na yi alkawarin zan ba harkar lafiya fifiko, ganin yadda Asibitocinmu na karkara suke da matsaloli, sannan zan ba da fifiko a kan iyayenmu mata masu juna biyu da kananan yara. Na fara da babban Asibitin da ke wannan Karamar hukumar, inda mai girma Gwamna Abdulaziz Yari ya zo ya kaddamar da wannan shirin nawa duk da cewa wannan Asibiti ba na Karamar hukuma ba ne, na jiha ne, duk da haka mu ka yi kokarin samar wa Asibtiin da Motar daukar marasa lafiya don a lokacin ba su da ita, sannan mun gyara masu motoci, da dakunan jinya, da na haihuwa, da gadaje, da wajen awon ciki da kuma gyara dakin likita mai ganawa da masu juna biyu, kuma mun sayo na’urori na bincike masu dauke da juna biyu, su ma dakunan kwanciyar kananan yara muka gyara shi, muka sanya gadaje, kuma muka kawo magunguna kyauta, da kuma Na’urorin gwajin jini da kuma rumbun aje jin duk muka sayo muka sanya a Asibitin. kuma mata da kananan yara magunguna kyauta ne ake ba su, kuma mai girma Gwamana ne ya zo ya kaddamar da wannan shirin. kuma tun daga wannan lokacin har zuwa yanzu shiri na nan na gudana.

Sannan kuma a duk Asibiti muna da gidauniya akan duk wata mai haihuwa da za a yi mata CS, za a yi mata shi kyauta, kuma a ba ta maganin kyauta. Haka nan kuma duk wani talaka mara galihu wand a kai ma aiki ko kwantar da shi muna da asusu a karshen wata za mu zauna da hukumar Asibitin mu tantace mutum nawa ya zo kuma daga ina ya ke, wane irin aikin a ka yi masa, idan tiyata ne ga shi a rubuce, idan kuma magani aka ba shi mu duba sai a biya kudin don duk wata haka muke yi. Har kawo yanzu.

 

Shin Wannan shirin ya takaita ne a babban Asibitin Tsafe, ko ya fantsama cikin sauran Asibitocin Karamar hukumar ?

Eh, lallai wannan shirin ya fantsama cikin asibitocin kananan hukumomi, a Asibitin ‘Yan kuzo akwai wannan shirin, kafin mu fara wannan shirin sai da muka gyara Asibitin gaba dayansa, sannan muka sanya na’urori, musamman dakin haihuwa, muka sanya Gadaje, da magunguna. Kuma mun yi wannan a Kuncin Kalgo da Asibitin Bilbis da Asibitin Gagazu.

Sauran Asibitocin da mu ke da su da dakunan shan magani, duk mun raba wadannan magunguna da inda muka gyara da inda ba mu gyara ba, kuma wannan ya taimaka wa mata ma su juna biyu ba sai sun zo Tsafe ba, ana ci gaba da ba su magani kyauta.

 

Shin wane matakin majalisarka ta dauka don ganin ba a yi wa wannan shiri zagon kasa ba?

A karkashin sashen Lafiya na Karamar hukumar, na sanya kwamitin da zai kasa ya tsare wajen ganin wannan shirin bai samu matsala ba, kuma ni ne Shugaban kwamitin, haka nan duk ma’aikacin da ya nemi ya kawo ma wannan shirin tangarda lallai majalisata ba za ta bar shi ba, don al’umma ya ke son hakarwa.

 

Wane kokari Karamar hukamar ke yi na samar da hanyoyi a fadin Karamar hukumar?

Babban alfaharina shi ne tunda muke al’umma ba ta taba amfana da kudin Kananan hukummomi ba irin wannan lokacin ba, don mai girma gwamna Abdulaziz Yari mun zauna da shi  a kan kudaden da muka tara na Asusun hadaka muka cimma matsaya kan ko wace Karamar hukuma a yi mata tituna kilomita Ashirin, amma tunanin mutane shi ne ayyukan ba za su yiwuba, don yadda aka dauko aikin, don a biyan kudin diyya na hanyoyin ruwa da za’a fitar, kuma cikin Kudirar Allah an kammala aikin, don mun samu karin kilomita biyar a cikin Karamar hukumar, mai girma Shugaban Kasa shi ne yazo ya Kaddamar da wannan aikin na Tsafe.

Kuma ita wannan gwamnati ta mai da hankali ne wajen fidda hanyoyi, da tituna ingantatu, Karamar hukumar Tsafe ta kasu gida biyu, akwai Tsafe ta Gabas, akwai ta Yamma, a Tsafe ta Yamma an yi tituna da ya tashi daga Wanke, Bawa ganga, Kwaren ganuwa, ya zo Keta, zuwa Danjibga, Kuncin kalgo ya fado Kuceri, wanda daga nan ne za ka kama hanya zuwa funtuwa. kuma lokacin da a kace za’ayi wannna titin mutane suna cewa, ba zaiyiyu ba, don an dade ana nema wannan hanya tun zamanin jamhuriya ta daya, sai gashi Gwamna Yari ya zo ya yi wannan titin inda a yanzu ya zama tarihi, wanda shi ma Shugaban kasa shi ne ya kaddamar da shi.

Bayan nan sai Tsafe ta gabas, shi ma an ba da kwangilar wannan hanyar don a shekarar 2015, sai aka samu tsaiko sabo da halin da tatalin arziki ya shiga, amma a yanzu a satin da ya gabata mai Girma Gwamna ya yi alkawarin ganin an fara wannan aikin a karshen watan hudu in sha Allah.

 

Wane kokari Majalisarka ke yi na inganta Tsaro?

Shi sha’ani na tsaro abu ne wanda ya shafi duniya ba ma Tsafe ba, don ya zama ruwan dare ne, don haka muna iya kokarinmu na samar da tsaro zuwa ga al’ummar mu da suke karkara, kuma kullum muna ta taruruka da Shugabannin al’umma da Sarakuna Hakimai Masu gari, da sarakunan Manoma da Fulani, da sauransu. A kullum da zarar wata matsala ta taso muna kokarin shawo kanta.

 

A karshe wane kira ka ke da shi ga al’ummar Karamar hukumar Tsafe ?

Kirana shi ne kamar yadda mu ke da hadin kai da son cigaba da kaunar juna mu kasance a haka, kuma mu kzama masu biyayya ga gwamnati, da kuma bin doka da oda da kuma addu’oin samun zaman lafiya, da ci gabanmu, da yi wa wannan gwamnati fatan alheri da mai Girma Gwamna Abdulaziz Yari addu’a akan Allah ya ba shi ikon kammala ayyukan da ya ke da kudirin yi ma wannan karamar hukuma ta mu, kuma ina godiya ga wannan jarida LEADERSHIP A Yau da ta zamo zakaran gwajin dafi a wannan kasa tamu ina godiya.

 

Exit mobile version