Connect with us

RAHOTANNI

Dalilinnmu Na Shirya Wa Yara Wasan Sallah A Musulunce –Binta Dorayi

Published

on

Kungiyar Mata musulmai na haraban ABU zariya jihad Kaduna ta shiryawa yara wasan sallah a musulunce.
Wakilinmu ya samu zuwa wajen wannan taro kuma ya bayyana yadda was an yaran ya gudana a tsari na add in in Islam.
Data farko dai taron wasan yaran an gudanar dashi ne a haraar babbar makarantar yara ta jami’ar A.B.U dake samaru zariya wato ABU staff school.
Daga cikin matakan da matan suka dauka shine, samawa wajan taron matakan tsaro mai karfin gaske karkashin hukumar tsaro na jamiar don kaucewa matsalar da ka iya tasowa.
Mataki na biyu kuma sun bayyanawa al’uma harajin shiga wannan wajen DA yakai kimanin #500 ga kowa uba KO yaro kuma lamarin ya sami karbuwa ta kowani bangare yaran da iyayen su.
Daga ciki abubuwan da suka bayyana wa jama’a akan wasan yaran shine Dan taimakawa yaran da fahimtar wasa a musulunce wanda hakan na kstwa yara hazaka tako wani bagare.
Bisa haka ne suka dauki mataki kamar haka, sunyi kokarin samun duk wani abun wasan yara da aka Saba amfani dashi wajen wasan yara a kasa baki daya amma babu wani abin dake nuna alaman tsiraici ko wani abu da ya kaucewa shari’ar Islama.
Abu na biyu kuma Wanda suka shirya taron sunyi bakin kokarin su wajen kaucewa wakokin zamani dake shagaltar da yara sai dai sun maye gurbin wakokin zamani Dda wakokin Islam wato (Islamic song).
Abu na uku shine sun kiyaye duk wani yaro shiga na banza , kuma sun kawo kayan wasa Kala Kala cikin harda Dokunan hawa Masu rai sabanin na robot da ake kawowa a wajan wasa yara a wasu guraren a wan nan wajen dokuna ne masu rai suka tanada har da masu kula dasu dan kiyaye lafiyar yaran.
Haka kuma sun samawa yara alkebba da ake shiga ta sarauta ga masu bukatar sawa.
Kuma wani abin sha’awa a gefe guda ga abinci kala-kala ga mai bukatar ci, a kyauta da lemun kwalba don kawata Wajen wasan.
Bagu da kari wannan wajen an kebewa iyaye runfa ta musamman don su kalli yaran su lokacin da suke gudanar da wasannin su cikin natsuwa .
Binciken da jaridar LEADERSHIP A YAU LAHADI tayi akan wannan wasan yaran a musulinci ya nuna cewa wannan wasan yaran shine na farko da aka taba shiryawa a zariya da jihar kaduna baki daya
Kuma daga cikin nasara da aka samu daya zama abin sha’awa shine
Samun amsa gayyatar iyaye da yara tare da bin dokar duk da aka tsara a wannan waje.
An samu cikakken nasara na fahintar da akeso yara su sama a yayin bikin sallah na man cewa dukkan Marsala da take samu a bangare gurbacewar tarbiya yara.
Haka yasa wakilinmu ya zanta da Amira ta wannan Forum din Hajiya Binta Aminu Dorayi akan sanin dadilin dayasa suka shirya wannan wasan yara a wannan lokacin.
Sai Amira ta kada baki tace ,” Abu na farko dai shine, kungiyarmu ta Muslim forum dake n ABU Zariya Forum ce dake gudanar da harkokinta duk bisa koyarwar Islama”
Amirar ta kara da cewa, basu takaita akan shirya wasan yara ba kawai sukan bayar da tallafi ga marasa karfi da marasa lafiya kuma sukan shirya taron karawa juna sani Dan taimakon juna akan abin da mukasan zai iya amfanar al’uma musulmi.
Hajiya Binta ta bayyana wa wkilanmu cewa, bisa tunanin da sukayi cewa da yawan lokutan bukukuwan sallah akan sami matsaloli da yawa na bata tarbiyar yara haka yasa sukai tunanin shiryawa yara wasan Sallah a kebe Dan kaucewa irin wancan Matsalar da ake fuskanta a yayin bukin sallah dan a lokacin bikin sallah akan sami Matsala na bacewar yara wani lokaci akan sace yara kuma ana samun yawaitar hadarin babur wato yan acaba suna buge yara kanana Wanda aka rasa rayuka da yawan kaski a yayin da yara ke gudanar da bukin sallah kuma mata gari na amfani da bukin sallah don yiwa yara Fyade a wasu guraren wanda hakan bai dace ba.
To bisa haka ne Amiran tace suka shirya wa yara wannan wasa dan kaucewa samun wata dabia Mara kyau da samun dabi’a ta gari .
Amirar ta kara da cewa, lokaciguda babu wani ko wata da zatazo da wata dabi’a mu zura idanu muna kallo a wajan wannan wasa saboda munsan haka yaranmu ya kamata su kasancea zo inda suke wannan wasa kuma babu wani halin banza mu Bari wan da haka ya kamata yaranmu su kasance.
Karshe Amiran tayi godiya ga dukkan wanda suka bada gudummawa har lamarin yasamu yiwuwa cikin nasara haka ta yabawa iyayen da suka amsa kiran su tace, kuma yanzu suka fara, na shakara mai zuwa zai fi na bana da yarddan Allah
Malama Salima na daya daga cikin Iyayen yaran da suka ziyara wannan wajen a nata bayani akan wannaan yara da Muslim forum suka shirya cewa tayi “Wallahi munji dadi sosai yaranmu sun sakata sun wala babu wani fargaba a garemu gashi muna kallansu suna kallon mu in an tashi zamu kwashesu mu koma gida ba tare da wata Matsala ba don haka muna Kira ga iyayen da aba wanda suka shirya wannan wasa na yara goyan baya nan gaba in sun sake shiryawa, mu kuma zamu cigaba da kowa yaran mu da yaddar Allah”.
Fatima Muhammad dalibace a staff School Kongo ABU zariya shekaran ta 8 tana daya daga cikin yaran da suke sami zuwa wannan waje itama ta bayyana ra’ayin ta na zuwa wanna waje Dan yin wasa da yara kanana kamar ta
Fatima tace “ Ban taba jin dadin wasa ba kamar yau ba dan na sami damar hawa Doki har yayi tafiya dani kuma shine na farko a rayuwata, ga banana da mamana suna kallona suna jin dad I nima Ina jin dad I don haka ma shekara mail zuwa zamuzo kuma Ina Kira ga yara yan’uwana muna wasa tare don haka ona kira ga rauran iyaye da basu samo zuwa a wannan lokacin ba shekara mai zuwa su yi kokari su zo da sauran kawayena don mu kulla zumunci Allah ya kai kowa gida lafiya sai wata sallah”.
An yi taro lafiya an tashi lafiya.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: