Abba Ibrahim Wada">

Dalot Ya Koma AC Milan

Kungiyar kwallon kafa ta AC Milan ta bauki aron ban kwallon tawagar Portugal, Diogo Dalot mai tsaron baya a Manchester United kuma Manchester United ta sayi ban kwallon kan fam miliyan 19 a watan Yunin shekara ta 2018 daga kungiyar FC Porto, inda ban wasan mai shekara 21 ya saka hannu kan yarjejeniyar shekara biyar da kungiyar a lokacin tsohon mai koyar da kungiyar Jose Mourinho.

Sai dai wasa baya Dalot ya buga wa Manchester United a bana shi ne a Caraboa Cup da suka doke Brighton amma idan za’a iya tunawa kwallon da ban wasan ya buga ne aka samu fenatin da Marcus Rashford ya buga ya ci da aka fitar da Paris St-Germain daga kofin zakarun turai na Champions League a watan Maris bin shekara ta 2019.

Lokacin da Manchester United ta bauki ban kwallon, Jose Mourinho ya kwatanta matashin ban wasan a matakin babu kamarsa a nahiyar Turai cikin tsaransa kuma ya buga wasa 23 a kakar farko da ya fara yi wa kungiyar kwallo, a kaka ta gaba kuwa da kungiyar ta bauko Aaron Wan-Bissaka, karawa 11 ya yi mata.

Advertisements

Har ila yau a wani labarin kuma kungiyar ta Manchester United ta kammala cinikin ban kwallon tawagar Brazil, mai wasa a kungiyar kwallon kafar ta FC Porto, Aleb Telles, sai dai daman tun farko United ta yi jan kafa wajen sayen mai tsaron bayan mai shekara 27 a duniya.

Ole Gunnar Solskjaer na neman kara karfin mai tsaron baya daga hagu, ya kuma tabbatar Telles ne zai share masa kuka da farko dai Porto na neman fam miliyan 18 daga United ga ban kwallon da yarjejeniyarsa zata kare a karshen kakar bana, wanda za a iya baukarsa a watan Janairu a matsayin mai cin gashin kai.

Telles wanda ya buga wa tawagar kwallon kafa ta Brazil wasa baya tal, ya ci wa Porto kwallo 21 a wasanni 127 da ya yi wa kungiyar kuma wannan labarin ya zo a lokacin da ake cewar United ta  kammala baukar ban wasan gaba Edison Cabani wanda bai da kungiya tun bayan barin Paris St Germain.

Exit mobile version