Dama Na San Zan Dawo Kan Ganiyata –Iheanacho

Leicester

Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Leicester City da Nijeriya Kelechi Iheanacho wanda ya dawo kan ganiyarsa ya dage cewa bai taba karaya ba game da yiwuwar komawa kan ganiyar tasa ko da kuwa a lokacin da duniya ta juya masa baya ne.

Iheanacho, mai shekara 24 a duniya bai samu gayyata daga kociyan tawagar Nigeriya ba domin buga wasannin karshe na neman cancantar shiga gasar cin kofin nahiyar Afrika ta 2022 bayan da ya tsinci kansa a tsaka mai wuya a kungiyar kwallon kafar Leicester City.

A watannin baya bayan nan lamura sun sauya game da shi inda aka ayyana shi a matsayin Gwarzon dan wasan kwallon kafar gasar Firmiya na watan Maris, kuma ya tsawaita zamansa a Leicester City zuwa kakar wasa ta shekarar 2024 haka kuma yana kan hanyar samun kyauta biyu a watan Afrilu.

dan wasan ya shaida wa manema labarai cewa yana ganin mutane da dama suna ganin ba shi da muhimmanci, amma bi taba yin kokwanto kan kwarewarsa ba kuma wannan matakin daya dauka shine yake taimaka masa a yanzu.

“Na shiga mawuyacin hali lokacin da komai ya tabarbare mini amma na yi aiki tukuru, kuma ina da manaja da sauran ma’aikata a Leicester Ciyu, sai dai abu mafi muhimmanci ina tare da dan uwa kuma abokina Wilfred Ndidi wanda ya rika karfafa mini gwiwa. In ji Iheanacho

Ya kara da cewa “Na yi matukar fuskantar kalubale amma yanzu ina cikin farin ciki komai ya sauya mini kuma ina taimakawa kungiya ta yadda yakamata domin samun gurbin zakarun turai na badi.”

Iheanacho shi ne dan kwallon da ya fi zura wa Leicester City kwallo a kakar wasa ta bana inda ya ci mata kwallaye 18 wanda hakan yasa kociyan kungiyar, Brendan Rodgers ya bayyana dan wasan a matsayin sabon dan wasa a kungiyar.

Cikin wadanda suka soki Iheanacho har da kocin Nijeriya Gernot Rohr wanda a bainar jama’a ya nuna kokwantonsa game da kwazon dan wasan da kwarewarsa a shekarar 2019 sai dai yanzu zai canja tunaninsa a kai.

Exit mobile version