Connect with us

LABARAI

Dambatta Ta Mori Ayyuka A Shekaru Biyar Na Gwamnatin Ganduje -Idris Zago

Published

on

Shugaban Karamar Hukumar Dambatta da ka jihar Kano, Hon Idris Haruna Zago ya bayyana cewa al’ummar Danbatta sun mori ayyukan ci gaba da dama tun daga zangon mulkin  Gwamnan Kano, Dokta Abdullahi Umar Ganduje na farko har zuwa wannan na biyu da ake ciki.

 

Shugaban ya yi nuni  da aikin asibitin Fagwalawa da aka yi musu wanda ya kai matsayin duk yadda ake so asibiti ya kai, an yi masa aiki mai inganci da tuni ake ayyukan kula lafiyar al’umma a cikinsa.

 

Alhaji Idris Haruna Zago ya ci gaba da bayyana cewa, a bangaren ci gaban matasa da mata da Gwamna Ganduje yake yi, su a Danbatta sun sami tagomashi sosai wajen cin gajiyar tsarin a fannoni da dama.

 

Shugaban ya kara da cewa an yi musu manyan kwalbatoci a Danbatta, sannan Gwamna ya sa an yi musu katafaren aiki a cikin babbar Kasuwar yankin ta dabbobi, musamman ma kasuwar tana taimaka wa Karamar Hukumar Danbatta wajen samun hanyar kudaden shiga na gudanarwa, duk kuwa da sau daya ta ke ci a mako.

 

Hon. Idris Haruna ya ce, dukkan ma’aikata da Gwamnati ke dauka a fannoni da dama su ma sun sami kasonsu daidai gwargwado sakamakon Karamar Hukumar Danbatta na daga tsofaffin Kananan Hukumomi, suna alfahari da hakan da godiya ga Gwamna Ganduje akan hakan.

 

Daga nan san Hon. Idris Zago ya bayyana irin hadin kai da goyon baya da Kwamishinan Kananan Hukumomi, Alhaji Murtala Sule Garo yake ba su wajen ci gabansu, inda ya ce abin karfafa gwiwa ne gare su.
Advertisement

labarai