Damfarar Intanet: EFCC Ta Cafke Mutum 60 A Akwa Ibom

EFCC

Hukumar yaki da rashawa reshen Uyo ta tabbatar da cafke mutum 60 daga shekarar 2017 zuwa yau, tare da gurfanar da mutum 37 a fadin jihar cikin wadanda ake zargi da damfara ta shafukan Intanet. Shugaban EFCC din reshen jihar, Garba Dugum ne ya bayyanawa manema labarai hakan a ranar Talata a garin Uyo.

Dugum, wanda wakilci mataimakin shugaban hukumar, Alex Ebbah ya ce hukumar ta su ta hada hannu da hukumar bincike ta FBI ta Amurka domin bankado masu aikata damfara ta Intanet. Dugum ya ce wannan umurnin ya fito ne daga bakin shugaban EFCC din na kasa, Ibrahim Magu inda ya bukaci da su gudanar da bincike na musamman domin bankado maboyar masu aikata irin wadannan aiki.

 

Exit mobile version