Daga Sagir Abubakar
An damfari wata maniyyaciya aikin hajji mai suna Hauwa Muhammad daga jihar Katsina har dala dari takwas a Madina da ke kasar Saudiyya.
Hauwa Muhammad wadda ta fito daga karamar hukumar kankara da ke shiyyar Malumfashi wanda ya damfare ta ya bayyana kansa a matsayin jami’in gwamnatin jihar Katsina.
Ta ce wanda ya damfare ta ya gaya mata cewa zai kara rarraba wa maniyyatan jihar Katsina dala dari inda ta ba shi ambulan dinta wanda yake dauke da kudadenta domin ya sa mata nata kason ciki.
Wadda aka damfara ta ce bayan da ya gudu sai ta ga dala tara kawai, suka yi saura a cikin abmulan din ta ta.
Amirul Hajji na shiyyar karamar hukumar Malumfashi, Alh. Yahaya ya bayyana ibtila’in a matsayin wani abu daga Allah.
Alhaji Auwal ya koka matuka kan cewwa masu damfara na zuwa da fasaloli daban-daban na yaudara inda ya gargadi maniyyatan da su kula sosai da irin wadannan mutane a kasa mai tsarki.