Musa Muhammad" />

Damina Uwar Albarka

08148507210   mahawayi2013@gmail.com

Bahaushe na cewa ‘Damina Uwar Albarka!’ Wannan magana ta Malam Bahaushe haka ta ke, domin a lokacin damina ne ake samun albarkatu masu yawa, musamman a fannin abinci, a lokacin ne ake samun abincin da ake ci, wanda kuma abinci ne jigon rayuwar kowane hallita. Kuma alhamdu lillahi, ya zuwa yanzu za mu iya cewa damina ta kankama, sai dai fatan Allah ba mu dacewa.

Duk da cewa a wannan zamani na damina, lokaci ne da ake samun albarkatu masu yawa, to haka kuma akwai wasu bala’o’i da sukan samu dan adam, wadanda a lokuta da dama ma har abin ya kan kai ga cin rayuka, baya ga asarar dukiya.

Damina ta kan kasance lokaci ne da ake samun raguwar munanan ayyuka, domin a shi lokaci ne ake samun matasa masu yawan gaske, wadanda suka tare a bariki, duk sun koma kauyukansu sun dukufa a harkar noma.

Wannan ne ma ya sa da zarar ruwan shuka ya sauka za a tarar da yawancin masu ayyukan karfi sun ragu, sun gona garuruwansu, hatta ma su almajirai masu karatun allo sukan ragu a bariki a daidai wannan lokaci, domin sun tafi garuruwansu domin yi wa Malaminsu noma, wasu kuma sukan tafi garuruwansu wajen iyayensu don taya su noma.

Shi ya sa ma a daidai wannan lokaci gwamnatoci ke samar da takin noma, kuma sukan yawaita kira ga jama’a, musamman matasa su koma gona, domin shi aikin gona yana zama wata babbar hanya ta samar da aikin yi.

Baya ga wadannan muhimman abubuwa masu amfani da Damina ke da su, akwai abubuwa, kamar yadda na fada a sama, masu hadari, wadanda ya wajaba a mayar da hankali wajen kiyaye su.

Don haka akwai matukar muhimmancin daukan matakan da suka wajaba don kare lafiyar jiki da ta dukiya da ta muhalli, musamman, domin akwai matakan da suka kamata a dauka don kauce wa kamuwa da cututtukan da ambaliyar ruwa, wanda wannan yanayi na Damina kan haddasa.

Lokacin Damina, za mu iya lokaci ne mai hadari, musamman wajen kamuwa da cututtuka ko ambaliyar ruwa, domin a lokacin ne ake samun yaduwar cututtuka daban-daban, musamman a yankunanmu na karkara da kuma wuraren da ba su da yanayin samun magudanan ruwa.

A wannan lokaci na Damina, akwai abubuwa da dama da suka wajaba a kula da su, amma dai muhimman abubuwan da za a fi mayar da hanakli, su ne samar magudanan ruwa, da kuma kariya daga cizon sauro. Wadannan abubuwa ne da galiban ake samun matsala da su a lokutan Damina, wadanda kuma su ne suka fi ba da wahala a rayuwar dan adam.

Domin rashin samar da magudanan ruwa suna haddasa mummunan ambaliyar ruwa, sannan akwai cututtuka masu hadari da akan kamu da su a sanadiyyar haka, musamman barkewar annobar kwalara, da kuma wasu cututtukan da su ma sukan faru a sakamakon wannan yanayi.

Shi ya sa ma duk lokacin da Damina ta karato, Hukumomi sukan ta yin kira a kiyaye zama a hanyoyin ruwa, kuma tana yawan kiran da a bubbude magudanan ruwa, tare da tsaftace wadanda ake da su ta hanyar rashin zuba rasha.

A duk lokacin da aka samu canjin yanayi, Likitoci da sauran ma’aikatan jinya sukan wayar da kan jama’a game da matakan da za a dauka don rage kamuwa da matsalolin da wannan yanayi kan jawo wa al’umma, musamman don ganin ba a samu wata matsala ba. Haka kuma sauran masana, musamman masana muhalli.

A irin wannan lokacin ne masana yanayin muhalli kan ta wayar da kan jama’a game da muhimmancin kiyaye ka’idojin da aka shata wajen kula da muhalli, inda har ma a wasu lokuta sukan yi jan hankali da gargadin cewa za a iya samun ambaliyar ruwa a wasu jihohi.

Masanan harkar lafiyar kuma sukan yi bayanin cewa a a wannan lokaci ana yawan kamuwa da cututtukan da suka hada da zazzabin cizon sauro, cutar kwalara da dai sauransu da dama.

Wani Likita da ke aiki a wani babban asibiti ya bayyana cewa a duk lokacin da aka shiga wannan yanayi, sukan samu karin marasa lafiya nunkin-banunkin wadanda suke samu kafin shigar yanayin, musamman a bangaren da cututtukan ke haddasawa.

Ya ce, a wannan lokacin Likitoci sukan shiga wayar da kan jama’a gadan-gadan don ganin sun samu wayewa kan yanayin da suka samu kansu, da kuma matakan da za su bi wajen kare kansu daga cututtukan da suke shiga jikin dan da kuma yana yin da akan samu ambaliyar ruwa a daidai lokaci irin wannan.

Likitan ya kuma bayyana cewa cututtuka na samun sakewa a lokacin Damina a jikin dan adam fiye da kowane lokaci, musamman zazzabin cizon sauro, da dai sauransu. Sannan kuma a wannan lokaci ne ake samun wani hatsabibin kuda da ke yada cututtuka da addabar jama’a.

Wannan ne ya sa nake ganin ya kamata Hukumomi da sauran kungiyoyin bayar da agaji na kasa da kasa, da sauran kugiyoyi da Hukumomin kasar nan da na duniya su shiga aiki wajen bayar da gaji, musamman na wayar da kan jama’a a wannan yanayi, musamman wajen binciken don gano wurare da aka iya samun ambaliya don su kiyaye.

Babban aiki ne da ke gaban Hukumomi, irinsu NEMA, SEMA, RED CROSS da sauran ma’aikatun kiwon lafiya da na jin kai na jihohi da na tarayya da ma sauran kugiyoyin kiwon lafiya masu zaman kansu, da masu kula da muhalli, su fito domin taimakawa wajen wayar da kai a wannan yanayi da muka shiga.

Haka su ma al’umma, yana da muhimmanci kowa ya zama ya dauki matakan kare kai, musamman wajen tsaftace muhalli, abinci, wurin kwana, tare da kuma kiyaye zama a kusa da rafuka ko manyan hanyoyin ruwa. Kamar dai yadda Hukumomi ke ta jan hankali.

Domin su cututtuka irin wadannan a kowane lokaci babu abin da ke yadasu cikin saurin kamar kazanta ko rashin tsafta ko kuma toshe magudanan ruwa, wannan kuma ita ce babban matsalar da ke damun al’ummarmu, musamman na yankunan karkara.

Haka kuma akwai jan aiki a gaban shugabannin addini wajen yin kira ga magoya bayansu wajen daukar matakan da muka lissafa a sama, da ma wasu da ba mu ambata a nan ba. Wannan kuwa ya zama wajibi ne bisa la’akari da irin muhimmancin da shugabannin addini ne da shi a tsakanin jama’a.

Muna addu’a, Allah ya kare mu daga kamuwa da duk wata cuta da za ta addabe mu, tare da neman kariya daga mummunar ambaliyar ruwan da za ta raba mu da muhallanmu. Amma dai yana da kyau a dauki matakan da suka dace.

 

Exit mobile version