Daminar Bana, Akwai Bukatar Gwamnati Ta Samar Da Wadataccen Takin Zamani Da Wuri

Takin Zamani

Daga Abubakar Abba,

A makon da ya gaga,  an ruwaito cewa,  samun kayan aikin gona na da matukar wuya,  musamman ganin cewa,  kakar aikin noma  ta  bana na kara kunno kai.

Hakan ya sa manoma sun fara nuna damuwarsu kan karin wahalar da suke aha ta samun kayan aikin gona,  musamman takin zamani wanda shi ne me a kan gaba wajen yin noma saboda tashinsa da kuma karancinsa.

Manoman sun yi nuni da cewa,  yanayin zai kuma kara janyo karancin kayan aikin na gona  a daukcin fadin kasar nan. Hakan dai ya biyo bayan yan watanni  da Ministan Ma’aikatar Aikin Gona da Raya Karkara Mohammed Sabo Nanono ya shelanta cewa,  ma’aikatarsa za ta janye daga sayowa da kuma sayar da takin zamani.

A tattaunawar da aka inda Sabo,  ya sanar da cewa,  daga yanzu,  ma’aikatarsa za ta rage rawar da take takawa wajen sa ido da kuma gindaya sharudda kan takin zamani.

Wannan furucin na Sabo ya janyo an ta yin fassata iri -iri akan shi,  inda wasu me ganin ko  gwamnati na son cire  tallafi a kan takin zamani ne.

Shugaban kungiyar manoma ta kasa (AFAN), Architect Kabiru Ibrahim a ha sa ra’ayin ya bayyana cewa, ya sane da cire tallafin a kan takin zamani  da gwamnatin tarayya ta yi,  inda ya kara da cewa,  ha by kuma wani abu da gwmnatocin jihohi za su iya yi kan lamarin.

Bugu da kari,  matakin na gwamnatin tarayya ya zo da bazata,  domin a ranar 7ga watan Disambar  shekarar  2020, Sabo ya bayyana cewa,  ma’aikatarsa, ta yi wa kimain kananan manoma miliyan biyar rijista yadda za su dinda samun takin zamani a cikin sauki a karkashin shirin samar da takin zamani na fadar shugaban kasa (PFI).

Sai dai, Ministan Ma’aikatar Aikin Gona da Raya Karkara Mohammed Sabo Nanono, bai yi cikakken bayani kana bin day a sa aka cire tallafin ba, yaushe ne aka yi hakan, kuma na wa ne aka tara kuma ina ne za a karkatar da kudin tallafin na takin zamani ba.

Har ila yau, ana ganin an dauki wannan matakin ne a cikin gaggawa ba kuma tare da an tuntubi masu ruwa da tsaki a fannin na aikin noma ba.

Bugu da kari, wannan maaatakin ya zo ba kan yadda ake son shi ba, musamman ganin ya zo daidai da daminar bana wacce tuni ta fara kankama a kuduncin kasar nan da kuma wasu sassan tsakiyar kasar, amma har yanzu, ba a samar da wadataccen taken zamanin ga manoman kasar nan ba.

Hakan ya kara jefa tsoron cewar, takin zamanin a kakar noman bana, zai zo kan kuraren lokaci, musaman idan aka yi dubi kan yadda farshin sa ke kara tashi.

Daga shekara 2016, a karkashin shirin na  PFI, an  sayar da takin zamanin mai nauyin buhun kilogiram 50 kan Naira 5,000 zuwa Naira 5,500.

Sai dai, a shekarar da ta gaba, farashin ya karu zuwa da yawa a daukacin jihohin da ke a kasar nan, an sayar da shi tsakanin farashin takin zamanin samfarin NPK Naira 6,700 zuwa Naira 8,000  sai kuma samfarin Urea daga Naira  8,800  zuwa Naira 13,000.

Exit mobile version