Dan Kasar Denmark Da Ya Yi Zanen Batanci Ga Annabi Ya Mutu

Dan jarida mai zaben shagube dan kasar Denmark Kurt Westergaard, wanda aka fi saninsa saboda zanen da ya yi na Annabi Muhammad (SAW) wanda ya janyo ce-ce-ku-ce, ya mutu. Ya mutu yana da shekarun 84.

Ya wallafa zanen ne a shekara ta 2006, kuma fafutikar da Musulmi masu raji suka yi ta kai ga zanga-zanga wadda ta rikide ta zamo tashin hankali a kasashe da dama a duniya.

A baya an yi hakon Westergaard don kashe shi, kuma ala tilas ya arasa rayuwarsa a wani mazauni na sirri tare da kariyar ‘yan sanda. An Sake wallafa zanen a mujallar nan ta zambo ta kasar Faransa wato Charlie Hebdo a shekarar 2015 ya sa an kai wa ofishinta hari inda masu kishin Islama suka kashe mutane 12.

Exit mobile version