Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Dan Kasuwa Ya Damfari Mai Sayen Fili Naira Miliyan 3

Published

on

Hukamar dake yaki da cin hanci da rashawa ta cafke wadansu ‘yan kasuwa mutum biyu Olufunmilade Adeyemi da kuma Oganla Oladimeji bisa zargin damfarar wani mai siyan fili Sanni Peters naira miliyan 3. Majiyarmu ta bayyana mana cewa ana zargin Adeyemi da amsar naira miliyan 3 daga wajen Peters domin ya saya masa fili guda 11 cikin rukunin gidajen da ba a kamala ba a Sangoted dake Jihar Legas. Lokacin da aka je wajen Ojiofor Blessing domin ya zama shaidan karya ga mai sayan filin na bogi. Wakilinmu ya labarta mana cewa bisa ga karan da hukumar ta gabatar, ya sa an kama Blessing. An dai gurfanar da su a gaban kotu dake Ikeja tare da kamfaninsu mai suna Stealth Communication Lmited  bisa laifin damfara.

Laifin dai ya saba wa sashi na 364 1) da kuma na 312 na kundin tsarin dokar Jihar Legas ta shekarar 2011.

An karanta karan kamar haka, “ sashin dokar Jihar Legas ta sami Olufunmilade Adeyemi, Aledander Moses da kuma kamfanin Stealth Communication Limited, da laifin amfarar Sanni Peters naira miliyan 3 domin su saya masa fili guda 11 a cikin rukunin gidajen da ba a kamala ba a yankin Sangoted dake Jihar Legas inda aka tabbatar da cewa karya ce”.

Lauyan hukumar EFCC mai suna Cleber Ibrahim ya bayyana wa kotu yadda Adeyemi da Oladimeji suka samu kudin amfaran ranar Litinin.

Lokacin da lauya N.A. Anana ya bayyana wa kotu shaida, Ibrahim ya gaya wa alkali  Olushola Williams cewa a shekarar 2016, hukumarsu ta samu karar da Ojiofor Blessing ya kai, sai ya hada mutanansa domin su gudanar da bincike kan al’amarin.

Ya kara da cewa wanda ake kara ya fara damfarar mai siyan filin ne tun lokacin da ya fara bayar da kudin. Ya ci gaba da cewa ranar 26 ga watan Yuli na shekara ta 2016 ne Oladimeji ya amsa naira miliyan 1.8 daga wajen Adeyemi.

Ya ce “lokacin binciken, ba mu samu Adeyemi a mazauninsa ba duk da irin kokarin da muka yi amma abun ya ci tura, sai hukumarmu ta ayyana cewa tana neman sa ruwa a jallo.

“A watan Maris na shekarar 2018, mun samu kira daga hukumar yaki da cin hanci da rashawa a kasar Ghana cewa sun cafke mutanan da muke nema ruwa a jallo. Mun garza ya zuwa kasar Ghana amma kafin mu kai, an riga an sake su.

“Mun samu rasarar kama Adeyemi da Aledander Moses a kasar Ghana amma ba mu samu Oladimeji. Lokacin da muka dawo da wadanda muka kama zuwa kasar Nijeriya, sai  daga baya muka samu rasar kama dayan wanda ake zargi”.

A bayanin da suka gabatar ga ofishin EFCC lokacin da aka kama su, sun amsa laifinsu amma daga baya lauyan da yake kare wadanda ake zargi ya karyata lamarin.

Alkali mai shari’a Williams ya daga sauraran shari’ar har sai zuwa ranar 26 ga watan Oktoba ta shekara 2018.

Advertisement

labarai