Dan kasar Kenya John Muiruri Mburu ne ya zama zakara a gasar gudun famfalaki ta duniya da ake yi a Kaduna bangaren tseren kilomita 21, kamar yadda kwamitin gudanar da gasar ya bayyanawa manema labarai.
An kaddamar da gasar ce mai suna Kaduna Marathon, wadda ta kunshi ajin tseren kilomita 10km da 5km da kuma 21kma, a ranar Asabar din data gabata duk da cewa an samu suka game da shiya gasar a wannan lokacin da ake samun matsalar tsaro a jihar.
An bai wa John Mburu dala dubu 10,000 (kwatankwacin kusan naira miliyan hudu) a matsayin kyautar zama zakara kuma kusan mutum 7,000 ne suka nemi shiga gasar ta Kaduna Marathon ta shekara ta 2020
A sauran azuzuwan gasar, Mohammed Sani Musa na Kaduna ne ya lashe gasar gudun kilomita 5km ita kuma Kangyang Solomon ta Jihar Filato ta lashe bangaren mata na gudun kilomita 10km, ya yin da dan shekara 15 Gyang Dabid ya lashe tserensa na farko a matakin kasa.
Wasu daga cikin manyan ‘yan wasan guje-guje da tsalle-tsalle da suka fafata sun hada da Shehu Mu’azu da Ismael Sadjo da kuma Danjuma Gyang sannan kusan mutum 7,000 ne suka nemi shiga gasar ta Kaduna Marathon 2020.
Gwanayen da suka fito daga kasashe irin su Kenya da Kamaru da Habasha da dai sauransu, na cikin shauki da farin cikin wannan gasa da za’a samu kyaututtuka sai dai an gudanar da wannan gasar a dai-dai lokacin da al’ummomi ke nuna damuwa kan tabarbarewar sha’anin tsaro a Kaduna.
To sai dai kwamishina mai kula da harkokin wasanni na jihar, Farfesa Kabiru Mato, ya ce gwamnatin jihar na daukar matakai na kare rayuka da dukiyoyin jama’a kuma hakan ba zai hana gudanar da wasanni ba a jihar.
Gwamna Nasir Elrufai ya ce gwamnati ta shirya wannan gasa ce domin nuna wa duniya irin albarkatunta a fannin yawon bude ido da kuma bai wa ‘yan kasa damar motsa jikinsu sannan akwai bukatar jaddada ko karfafa hadin-kai da zaman lafiya tsakanin al’umomi, kuma gasa irin haka na habbaka tattalin arziki da taimaka wa matasa, da kuma zaburar da mutane kan kula da lafiya, in ji gwamnan.
Gwamnan ya kuma kara da cewa za’a samu shigowar baki daga sassa daban-daban na duniya domin yawon bude ido bugu da kari ya nemi hadin-kan ‘yan jihar domin ganin an gudanar da gasar cikin raha da annashuwa, da kuma karfafa gwiwar masu shiga tseren da jami’ai.
Gwamnatin Kaduna dai ta tabbatar da cewa akwai mutane sama da 80 da suka gwanance a gudu ‘yan Najeriya da suka shiga gasar sannan kuma an rarraba yadda za’a gudanar da gasar zuwa gida uku, akwai rukunin ‘yan tseren kilomita 21 da masu yin kilomita 10 da kuma kilimota 5 a bangaren maza da kuma mata.
Sannan gwamnati ta sanar da cewa za’a rufe wasu tituna cikin garin Kaduna daga karfe 6.00am na safe zuwa 3.00pm na yamma domin tabbatar da tsaro da nasarar gasar wanda kuma tuni an yi lafiya an gama lafiya.