Dan wasan baya na Arsenal, Gabriel sakamakon gwaji an tabbatar da kamuwarsa da cutar korona, hakan zai ja mishi kin buga wasa a karawarsu da kungiyar Brighton da West Brom.
Arsenal ta fitar da wannan sanarwa ta shafin yanar gizonta a ranar Alhamis ce Wa “Gabriel ya kamu da cutar korona kuma yanzu haka yana kebe bisa ka’idojin da Gwamnatin Burtaniya da Premier League suka gindaya.”
“Za mu ci gaba da sanya ido da tallafawa Gabriel, kuma muna fatan zai sake samun damar cigaba da wasa damu bayan wasanninmu biyu masu zuwa,” inji sanarwar.