Connect with us

LABARAI

Dan Majalisa Ya Bukaci NEMA Ta Agazawa Wa Al’umma Duguri Bisa Barnan Da Guguwa Ta Yi Musu

Published

on

Wani dan majalisar wakilai Dakta Muhammad Sani Abdu ya yi kira ga hukumar samar da agajin gaggawa wato NEMA da ta kawo tallafi wa jama’an kauyen Duguri wadanda guguwa ta yi wa mummunar barna a kwanakin baya.

Dakta Sani Abdu wanda shine ke wakiltar mazabar Alkaleri/Kirfi a majalisar wakilai ya mika koken ne a sa’ilin zaman majalisar kan bukatar kawo dauki a wannan yankin na Duguri da ke karamar hukumar Alkaleri.

Ya bayyana cewar mutane biyu sun halaka a lokacin da guguwar ta yi barnan, wanda kuma ta lalata gidaje sama da dari biyu gami da dukiya na miliyoyin naira, hade da makarantun gwamnati guda takwas, fol-fol na wutar lantarki, cocina, massalatai, salwantuwar shano da wasu kayyakin dukiyar jama’an Duguri.

Wakilinmu ya labarto cewar guguwar wacce ta auku tun a ranar Laraba 2/5/2018 inda ya yi barna wa gidaje sama da dari biyu massalatai, cocina, makarantu sama da dari biyu ne ne suka fadi inda suka rushe a sakamakon wannan mummunar iskar.

Sarkin Duguri, Hakimin Kasar Duguri Alhaji Ibrahim Y.M Baba ya bayyana irin ta’addin da Iska da ruwan suka yi wa jama’ansa a wannan ranar ta 2/5/2018 yana mai bayanin cewar an samu rushewar gidaje, masallatai, cocina, dabbobi da sauran ababen da suka salwanta a sakamakon wannan hatsarin da ta auku musu.

Sarkin ya bukaci agajin hukumar samar da agajin gaggawa domin rage wa jama’an da suka samu wannan ibtila’in sauki domin taimaka musu.

A lokacin da gwamnan jihar Bauchi Muhammad Abdullahi Abubakar ya kai ziyara kauyen domin gani da idonsa irin barnar da Iskan ya janyo wa kauyen wanda ya kai ga rusa kauyuka har guda 13 gami da kashe mutane uku a kauyen na Duguri, gwamnan ya nuna jimaminsa hade kuma da shan alwashin taimaka wa wadanda ibtila’in ya auku musu.

Wakilinmu ya labarto cewar guguwar dai ta barnata Gundumomin da suka hada da Yali, Bandibit, Gaji, Bun, Bayak, Kunzun sauran kauyukan su ne Tummi, Nyalam, Tonlon, Bajoga da kuma Taksamat.

Sai kuma a Gundumar Dan da ke Duguri inda iskar ya ruguza kauyuka biyu masu suna Sharan da kuma Dangudi wadanda dukkaninsu yanzu haka guguwar ta yi musu waja-waja.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: