Dan Majalisa Ya Yi Kira Ga Iyayen Yara A Katsina

Yara

Daga Sagir Abubakar,

A wani cigaban na dan majalisar dokokin jihar Katsina mai wakiltar karamar hukumar Katsina ya yi kira ga iyaye da su ja kunnen ‘ya’yansu dangane da ta’amuli da miyagun kwayoyi.

Alhaji Aliyu Abubakar Albaba ya furta haka ne a wajen bikin yaye dalibai (42) arba’in da biyu wadanda suka samu horon sana’o’in hannu wanda wata kungiya wadda ba ta gwamnati ba ta shirya anan Katsina.

Yayi kira ga jama’a da su rika sayen kayayyakin da ire-iren wadannan dalibai ke yi. Shi ma da yake magana, mai ba gwamna shawara na musamman akan cigaban matasa Ibrahim Aminu ya jaddada bukatar dake akwai ga matasan jihar nan na su rungumi sana’o’in dogaro da kai.

Ya yi kira ga sauran kungiyoyi da suyi koyi da wannan kungiya wadda ba ta gwamnati ba wajen samarwa matasa abin yi.

Tun farko shugaban kungiyar Alhaji Aliyu Salmanu yace daliban sun koyi yadda ake yin zanen gado, da takalma da jikkuna da dai sauransu. Wasu daga cikin daliban da aka zanta dasu sun godema kungiyar akan shirya horon, daga bisani kuma an basu takardar shedar kammalawa.

Anyi kira ga iyaye a Katsina dasu tabbatar da yaransu na bin dokoki da ka’idojin da aka gindaya don kare yaduwar cutar corona.

Sakataren ilimi na karamar hukumar Katsina Alh. Mannir Yahaya ya bayyana hakan a yayin da yake ganawa da manema labarai a ofishinsa.

Kamar yadda yace hakan zai taimakawa kokarin gwamnati na yaki da yaduwar cutar.

Alh. Mannir Yahay ya kara da cewa an dauki kwararan matakai na tabbatar da kare dalibai da malamai daga kamuwa da cutar.

Yace an sanya dokar amfani da abin rufe baki da hanci a farfajiyar makaranta tare da samar da ruwan da abin tsabtace hannu a kofar shiga makarantun don kare yaduwar cutar.

Sakataren ilimi ya tinaso cewa an tsabtace makarantu kafin yara su fara karatu.

Alhaji Mannir Yahaya ya kuma bayyana cewa anyi tsarin rage cinkoso ta yadda daliban aji 1,2,3 zasu dauki darasi da safe a yayin day an aji 4,5,6 zasu dauki darasi da marece.

Exit mobile version