Da yammacin ranar Larabar da ta gabata ne Honorable Muhammad Aminu Tukur ya sanar da ficewarsa daga cikin jam’iyyar APC, bayan fitowarsu daga wata ganawa da jam’iyyar APC da kuma masu neman APC ta tsai da su a matsayin ‘yan takarar cike gurbin Sanatan Bauchi ta Kudu, lamarin ya biyo bayan kin amince da gudanar da zaben fid da dan takarar APC na sabon tsarin kato-bayan-kato kan wannan zaben.
Bayan nan, a daren ranar kuma ya ayyana shiga cikin jam’iyyar Action Peoples Party (APP) domin ci gaba da neman kujerar Sanatan Bauchi ta Kudu.
Muhammad Aminu Tukur wanda yanzu haka dan majalisa ne da ke wakiltar al’ummar mazabar Lere/Bula a majalisar dokokin jihar Bauchi, ya dai samu nasarar lashe zaben fid da gwani na jam’iyyar APP bayan shigarsa cikinta a wannan ranar.
Da yake bayyana wa manema labaru dalilansa na daukar wannan matakin, Malam Aminu Tukur ya nuna rashin gamsuwarsa ne kan yadda gwamnatin jihar da kuma jam’iyyar APC a jihar suka ki bin umurnin da shugaban jam’iyyar APC na kasa ya bayar dangane da gudanar da zabe kato-bayan-kato.
Ya nuna cewar rashin yin hakan tabbas babbar rashin adalci ne a gare su, domin a cewarsa an rigaya an mallaki wakilai gudanar da zaben wato ‘Delegate’ Tukur ya shaida cewar yin hakan zai bashi dama da shi da magoya bayansa su samu nasarar cim ma burinsu.
Ta bakinsa, “Mun shiga cikin jam’iyyar APP mai alamar Giwa mai kirarin nasara. Sanin kowane dukkanin matakan da suka dace domin a yi mana adalci a bisa alkawarin da ke tsakaninmu da shugaban jam’iyyar APC na kasa Kwamared Adams Aliyu Oshomhele wanda ya tabbatar mana da cewar za a yi zabuka a bisa kato bayan kato; wanda kuma su wadanda suka zo gudanar da wannan zaben fidda gwani na jam’iyyar APC don tunkarar neman cike gurbin Sanatan Bauchi ta Kudu suka muzanta wannan, sun yi abin da suke so.
“Abin da muka fada a gabansu shi ne mu ba mu yarda da shugabancin da ake da shi a halin yanzu a jam’iyyar APC jihar Bauchi ba,” in ji Tukur
Ya bayyana cewar tun bayan gudanar da zaben gundumomi na jam’iyyar APC a matakin jihar Bauchi sun baiwa shugaban jam’iyyar na kasa sharuda guda uku wanda in ana son su ci gaba da zama a cikin jam’iyyar dole a cike musu, amma hakan ya gagara, daga cikin har da batu soke zaben jagororin APC na gunduma, kananan hukumomi da na jihar Bauchi, na biyu sun nemi a yi kato bayan kato a cire amfani da delegate a wajen fidda dan takara.
Honarabil Aminu Tukur ya bayyana cewar wannan sauya shekar da ya yi zai ba shi zarafin kai wa ga nasara don samun hadewa wannan kujerar, “yawan mutane shine ba wai tarin rumfuna ba, muna da yawan mutane domin muna da magoya baya sosai. Duk inda muka bi magoya bayanmu za su biyu,” In ji shi
Jam’iyyar ta APP ta zabi Aminu Tukur a matsayin wanda ya ci zaben fidda gwani na jam’iyyar ta APP don neman wannan kujerar na cike gurbin Sanatan Bauchi ta Kudu, a lokacin da ke jawabi a wajen, shugaban jam’iyyar ta APP Kabiru Abdullahi Shuwa ya shaida a wajen zaben wanda ya gudana a dakin taro na makwancin Sa Abubakar Tafawa Balewa ya ce wannan alamin samun nasarar jam’iyyarsu ne, yana mai shaida cewar za su kai ga nasarar mallakar wannan kujerar.
Da yake tsokaci, wani abokin siyasar Aminu Tukur, Sani Shehu wanda aka fi sani da Sanin Malam ya bayyana gazawar gwamnatin jihar Bauchi da jam’iyyar APC a jihar wajen fitar da tsare-tsaren da suka dace da muradin magoya bayan jam’iyyar, yana mai shaida cewar hakan kuma zai kai ga rugujewar jam’iyyar.
Ya taya dan uwansa murnar cin zaben fidda gwani da jam’iyyar APP din ta yi, inda yanzu haka aka za bi Aminu Tukur don ya wakilci jam’iyyar a zaben da za a fafata a ranar 11 ga watan Agustan don cike gibin Sanatan Bauchi ta Kudu wanda ya rigamu gidan gaskiya a watannin baya.
Tun da fari ma, dan takarar Aminu Tukur ya yi riga-kafin masu cece-kucen cewar duk wadanda suka fita daga APC ba masoyan Buhari bane, ya ce “Duk yadda wani masoyin Buhari ya kai na kai, amam rashin adalcin da ke cikin jam’iyyar APC a jihar Bauchi tura ta kaimu bango dole mu fice, amma mu masoya Buhari ne,” In ji Tukur
Yanzu dai Aminu Tukur shine ya zama dan takarar APP a zaben cike gurbin da za a yi. INEC dai ta ware ranar 11 ga watan Agustan 2018 a matsayin ranar gudanar da wannan zaben.