Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Dan Mawaki Dbanj Ya Rasa Ransa A Kududdufin Ninkayan Gidansa

Published

on

An ruwaito cewar, yaro dan watanni sha uku da ya fada wajen wanka dake dake a gidan sanannen mawakin D’banj nan dake yankin Ikoyi a cikin jahar Legas, ya fada ne a lokacin da wasu abokai na mawakin suka kai ziyara a gidan.
A lokacin da lamarin ya auku D’banj ya yi tattaki zuwa yankin Los Angeles dake kasar Amurka don halartar wani taron bayar da lambar yabo ta waka.
Sai dai, mawakin har yanzu bai fitar da wata sanarwa ba akan lamarin amma ya fitar da wani sako a fajin sa na Instram a ranar lahadin data gabata, inda wasu sanannun suka dauki hakan a zaman martanin day a mayar akan lamarin.
A hoton da ya yada, ya rubuta ya nuna juyayin sa akan lamarin inda ya ce hakan wani gwaji ne kuma Allah shine ke yin komai.
Mabiya mawakin da dama sun taya mawakin ta’aziyyar lamarin.
Sanata mai wakiltar mazabar Bayelsa ta yamma Ben Bruce ya yi wa mawakin ta’aziyya da cewra ya rungumi kaddara.
Acewar sanatan, “ ina yi bakin ciki akan samun labarin mutuwar dan ka na farko domin mutaw da tana da cin rai da kuma zafi matuka.
Suma sauran mawaka kamar su Tiwa Sabage, Michael Ajereh da akafi sani da Don Jazzy da Folarin Falana da aka fi sani da Falzdbahdguy da Funke Akindele da Olamide Adedeji da Omotola Ekeinde da Jackiah Appiah da Genebiebe Nnaji da Peter Okoye sda akafi sani da Pskuare da Olubankole Wellington da akafi sani da Banky W da Toke Makinwa da kuma sauran su, dun sun jajantawa mawakin.
Acewar Sabage, “ a cikin watan da wuce ina rungume da yaron don taya shi zagayowar ranar haihuwar sa, wannan mutuwar ta yaron ta girgiza ni kuma tana da wuyar jurewa.”
Shi kuwa Ajereh a nashi ta’ajiyyar ya ce, “ labarin lamarin ya girgiza shi sosai da fatan Allah zai tausashi zuciyar D’banj da kuma mutanen gidan sa .”
Ita kuwa Nnaji ta ce, “ ku taya ni yin addu’a don taya Oyebanjo ta’aziyya a wanan lokacin duk da cewar baza mu san jin zafin rashin kowa ba amma addua’a ko yaya take zata taimaka.”
Shi kuwa Wellington ya ce, a wannan yanayin sanin kalmar da za’a yi amfani da ita don yin addu’a tana da wuya, amma da fatan Allah zai tausashi zuciyar iyayen yaron.
Haka Jalade, “ mene wannna na ke ji haka? Amma addu’ar mu da kuma tunanin mu a wannan lokacin D’banj, tana tare da kai.
Sai dama wasu yan Nijriya masoya mawakin ta karfar su ta yanar gizo akan gina wajen wankan ganin irin hadarin dake tattare da hakan a gidan sa.
Wani mai suna Tobi Samson a fajin sa na Twitter ya bayyana cewar bkimanin masoyan mawakin su dari bakwai ne suka gargade shi akan gidan wajen wankan saboda yanayi na tsaro.
Ya kara da cewar, ba sau daya ba ba kuma sau uku ba, masoyan mawakin a cikin sati biyar da suka wuce bayabn sun ga faifan bidiyon wajen wankan da mawakin ya yada sun gargade shi akan hadarin dake tattare da gina wajen wankan a gidan sa kuma a lokacin yaje kusa da wajen wankan dauke da dan nasa.
Akwai wani daga cikin masoyan mawakin mai suna Koji da yaga faifan bidiyon har ta kai ga ya gargadi mawakin cewar yabi a hankali, inda ya kara da cewar don Allah ka tabbatr akwai wasu a gidan ako da yaushe.
Shima wani masoyin mawakin a fajin sa na Instagram @mad_tunde_mamediarra_mbaye, ya gargadi mawakin da yabi a hankali domin yaron zai iya fadawa cikin wajen wanka.
Wata majiya ta ce, an sanar da jami’an ‘ yan sanda lamarin, sai dai har yanzu kafafen yada labarai basu buga labaran ba amm sai dai har yanzu yan sanada suna kan binike akan abinda ya haddasa aukuwar lamarin.
Kakakin yada labarai na rindinar yan sanadan jahar CSP Chike Oti, a sanarwar da ya fitar ya ce, kwamishinan yan sandan jahar Edgal Imohimi, ya jajanta akan mutuwar.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: