Connect with us

LABARAI

Dan Nijeriya Ya Zama Shugaban Jami’ar Leeds Ta Ingila

Published

on

Shahararren Malamin Jami’a dan Nijeriya, Farfesa Charles Egbu ya zama sabon shugaban jami’ar Leeds Trinity da ke kasar Ingila. A sanarwar da jami’ar Leeds Trinity ta fitar a shafinta na yanar gizo, ta bayyana cewa Farfesa Charles Egbu zai gaji Margaret House wacce za ta sauka daga kujerar.

Farfesa Margaret House ta shafe shekaru bakwai a matsayin shugabar wannan jami’a ta Leeds Trinity. Farfesa Charles Egbu zai koma birnin Leeds da ke Ingila ne domin ya karbi ragamar makarantar da ya yi karatu, ya kuma taba yin aikin koyarwa.

Farfesa Egbu zai fara aiki a ofis a ranar Lahadi 1 ga watan Nuwamban 2020. Egbu ya yi magana bayan an zabe shi a matsayin shugaban jami’ar, inda ya ce: Na yi farin cikin samun aiki da jami’ar Leeds Trinity; wanda manufofinta su ke kai dalibai ga samun nasara a rayuwa, kuma su ka dace da irin nawa manufofin. Jami’ar ta na da tsawon tarihin karatu, koyarwa da aiki, ina farin cikin daurawa daga ginin da Farfesa House ta samar.
Advertisement

labarai