Daga Muhammad Sani Chinade Damaturu
Wai Hausawa na cewa gado ba karambani ba Leadership A Yau ta samu tattaunawa ta musamman da wani yaro dan kimanin shekaru 10 a duniya da ya fara sana’ar fede dabbobi tun yana dan shekaru 8 a duniya mai suna Sani Ibrahim Baushe mazaunin garin Damaturu a jahar Yobe, wanda saboda karantar jikinsa, da ka gan shi za ka tsammanci bai wuce shekara takwas ba amma kuma a hirarsu da Leadership A Yau a lokacin da yake kan aikinsa ya tabbatar da cewa a kullum in dai ya samu aikin fede dabbobi ya kan iya fede akalla dabbobi 5 zuwa bakwai lokaci guda ba tare da ya gajiya ba. A sha karatu lafiya.
Yaya aka yi ka fara wannan sana’a ta fida duk da yake ga ka da karancin shekaru, kana ga ka kuma mai karamin jiki matuka?
To ni dai kamar yadda kake gani na wannan sana’a ta fede dabbobi gadar ta na yi wajen mahaifina domin kuwa mu mahauta ne, kuma tun ban kai haka ba nake bin mahaifina in zai tafi aikin fede dabbobi ina masa tokari, don haka ina ganin irin yadda yake yi har kuma na kai kimanin shekaru 8 sai nima na fara gwada aikin na fida da kaina har kawo ya zuwa yanzu da na
Duk da cewa, ga shi kai karamin yaro ne wanda bai kai minzilin karfi ba amma kuma duk da haka dabbobi nawa kake iya fedewa a kullum in har ka samu aikin?
To a gaskiya in dai na samu aikin nakan iya fede dabbobi akalla biyar zuwa shida ba
kuma tare da na gajiya ba, kuma cikin ikon Allah a cikin kankanin lokaci zan iya fede su ba kuma tare da na nemi tallafin kowa ba, domin a shekarar bara lokacin sallar layya kafin lokacin ya wuce a kullum nakan fede dabbobi shida zuwa sama da hakan, don saboda ma karantata da kuma karancin shekaru na har jama’a kan yi ruguguwar kira na domin in musu fida saboda sha’awar ganin yaro irina amma kuma na iya yin sana’ar da an fi zaton manya ne ke iya yin ta. Domin a sallar layyar bara ba zan manta ba wani ya sa a kira masa wanda zai fede masa ragon layyarsa sai aka kira ni da aka kira ni, da wannan mutumin ya gan ni sai ya ce, shin wai ni ne zan yi fidar ko kuma babana ne? Sai na ce ai ni ne zan yi, sai ya ce to amma kar fa in bata masa fatar ragonsa saboda yana tantamar ko ba zan iya ba. Amma abin ka da sababbe nan da nan yana tsaye sai ga shi na fede masa ragon nasa sarai ba tare da na bata masa fatar ba saboda jin dadi sai mutumin nan da ya daga ni sama kana kuma ya biya ni fiye da yadda aka saba biyana.
Ko tunda ka fara yin wannan aiki yau kusan skekara 3 ko ka taba cin karo da wata
matsala musamman ganin cewa, fidar dabba sai da hikima gudun kar a bata fata?
A hakikannin gaskiya tunda na fara fida ban taba cin karo da wata matsala ba, balle har na nemi tallafin wani illa dai na san a mafi yawan lokaci wasu daga cikin kanne na kanana sukan bi ni aikin su kuma taya ni rike dabbar don fedewa, hakan ba wai don ba zan iya fedewa ni kadai ba ne, sai dai don su ma su koya kamar yadda ni ma a baya na rika bin mahaifina aiki har kuma na koya.
Daga fara wannan aiki na sana’ar fida zuwa yanzu ko ka yi wani abun kanka?
kuma keken hawa irin namu na yara da kuma suturu da nake saya a kaina da kuma kannena, har ma a wasu lokuta nakan tallafawa iyayena da dan wani abu cikin wannan sana’a ta fida.
Ko a halin yanzu akwai a cikin sa’o’inka wadanda suka fara gwada wannan sana’a ta fida?
A duk fadin unguwarmu ta Fawari ban yi tsammani akwai wani yaro kamar ni da ya fara irin wannan sana’a ba, domin gani suke yi kamar ba za su iya ba, shi ya sa ma nake kiransu da su yi koyi da irin yadda nake yi.