Yusuf Shuaibu" />

Dan Shekara 60 Ya Yi Wa ’Ya’yansa Guda Biyu Fyade

A ranar Talata ne, kotun alkalin kotun Ikeja ya daure wani mai sayar da maganin gargajiya dan shekara 60, mai suna Taiwo Ilesanmi a gidan yarin Kirikiri, bisa yi wa ’ya’yansa guda biyu fyade. Alkali mai shari’a P. E. Nwaka, ya bayar da umurnin a cigaba da tsare Ilesanmi a gidan yari, har sai an samu shawarwari daga daraktan watsa labarai na kunguyar loyoyi na Jihar Legas. Nwaka ya dage sauraran karar har sai narar 13 ga watan Yuni.
Wanda ake zargin ya musanta laifin da ake tuhumar sa da shi.
Shi dai Ilesanmi yana zaune ne a gida mai lamba biyu da ke kan titin Kulade cikin yankin Abesan ta Ipaja kusa da Jihar Lagos, ya na fuskantar tuhumar tozarci da kuma laifin fyade.
Tun da farko dai, lauya mai gabatar da kara, Christopher John, ya bayyana wa kotu cewa, wanda ake tuhuma ya fara aikata wannan laifi ne tun a shekarar 2013 da kuma watan Afrilun shekarar 2019. John ya kara da cewa, wanda ake ya kai shekara shida ya na lalata da diyarsa guda biyu masu shekaru 10 da 14. “Su dai yaran ba za su sake zama da wanda ake tuhumar ba, yarinyar mai shekaru 14 ce, ta bayyana wa wata makwabtar labarin lamarin, inda ita kuma ta kai rahoto a ofishin ‘yan sanda.”
John ya ce, yaran sun fada wa ‘yan sanda cewa, wanda ake tuhuma ya na yin lalata da su ne duk sanda matarsa ba ta nan, ya kuma yi musu barazanar zai kashe su idan suka fada wa wani lamarin lamarin. “An cafke wanda ake tuhuma, sannan aka gurfanar da shi a gaban kotu.”
Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya ya ruwaito cewa, wannan laifi dai ya saba wa sashi na 137 da 260 na dokar manyan laifuka ta Jihar Legas ta shekarar 2015, inda ta tanaji hukuncin daurin raid a rai a gidan yari ga duk wanda aka samu ya aikata irin wannan laifin.

Exit mobile version