Yusuf Shuaibu" />

Dan Shekara 82 Ya Bukaci Kotu Ta Hana Matarsa Dukan Sa

Wani dattijo mai suna Godwin Akinola dan shekaru 82, ya gurfana a gaban kotun Agege da ke Legas, inda ya bukaci kotu da raba aurensu tsakaninsa da matarsa wacce su ka kwashe shekaru 30 tare, ya kuma bukaci kotun ta hana matarsa dukansa har lokacin da za a raba aurensu. Shi dai Akinola ya na zaune ne a yankin Ogba da ke cikin Jihar Legas, ya dade ya na neman a raba aurensu tsakaninsa da matarsa mai suna Anthonia, ya na so a raba wannan auren ne sakamakon farmaki da matarsa da ke kai masa. “Matana masifaffiya ce,” in ji shi.
Sai dai kuma dattijon ya nemi kotu ta ba su lokaci ko za su iya shawo kan matsalar da ta ke tsakaninsu. “Tun da na kawo lamarin zuwa wannan kotu mai adalci, ina bukatan a ba mu lokaci ko za mu iya zama lafiya da matana. ‘Yan’uwanta sun roke ni a kan in yi tuhani wajen bukatar raba aure a tsakanin mu duba da yanayin shekaruna. “Mu na da yaro mai shekara 35. Ina bukatar kotu ta hana mata duka na har lokacin da za a yanke hukunci,” in ji shi.
Alkali mai shari’a Misis Patricia Adeyanju, ta shawarci ma’auratan da su zauna lafiya a tsakaninsu. Ta dage wannan sauraron karar har zuwa wani lokaci.

Exit mobile version