Dan wasan gaban kungiyar kwallon kafa ta AC Milan, Rafael Leao ya ci kwallo mafi sauri a tarihin gasar Serrie A a ranar Lahadin data gabata, bayan da a cikin dakikoki 6 ya sanya kwallo a ragar kungiyar Sassuolo a wasan da suka doke ta 2-1, abin da ya kai AC Milan saman teburin gasar, a gaban Inter Milan.
kungiyoyin AC Milan da Inter Milan ne wadanda ke kokarin samun nasarar lashe gasar Serie A ne a karon farko tun bayan shekarar 2011, kuma AC Milan ta kaddamar da hari ne daga bangaren dan wasan tsakiyarsu, dan kasar Turkiya Hakan Calhanoglu, wanda ya saka wa Leao kwallo shi kuma bai yi wata wata ba ya antaya ta cikin raga
A baya dai kwallo mafi sauri da aka taba ci a gasar it ace wacce shahararren dan wasan tawagar kwallon kafar Italiya Paolo Poggi ya ci wa kungiyar Piacenza a wasansu da Fiorentina a watan Disamban shekarar 2001 bayan dakikoki 8.
AC Milan na gaba da Inter Milan, tawagar Antonio Conte, da ta doke Spezia 2-1, da maki guda daya, tazarar maki 4 ne tsakaninsu da Jubenus, wadanda suka lallasa Parma da ci 4-0 a ranar Asabar.