Connect with us

WASANNI

Dan Wasan Kano Pillars Gambo Muhammad Ya Koma Kasar India

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta East Bengal dake arewacin kasar India ta tabbatar da siyan dan wasan gaba na  kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars Gambo Muhammad domin ya bugawa kungiyar wasannin kakar wasa ta shekara ta 2018 zuwa 2019.

Gambo, wanda yana daya daga cikin ‘yan wasan gaba da sukafi zura kwallaye a raga a gasar firimiyar Najeriya ya amince da kwantaragin shekara daya da kungiyar ta India kuma tuni kungiyarsa ta kano Pillars ta tabbatar da zancen.

Dan wasan wanda ya lashe gasar firimiyar Najeriya sau uku da kungiyar ta Pillars cikin shekaru goma da yayi a kungiyar ya kuma wakilci kungiyar a wasannin gasar cin kofin zakarun nahiyar Africa inda kungiyar taje wasan kusa dana karshe a shekara ta 2008.

Gambo mai shekara 30 a duniya ya fara bugawa tawagar Najeriya ta Super Eagles wasanni ne a shekara ta 2012 ya buga wasanni 7 sannan ya wakilci Najeriya a gasar cin kofin Comfidaration da aka buga a shekara ta 2013 a kasar Brazil.

“Abin farin cikine kasancewa a babbar kungiyar kamar wannan kuma ina fatan cigaba da zura kwallo a raga kamar yadda nasaba a baya domin taimakawa kungiya ta taje inda yakamata a gasar da zamu fara bugawa” in ji Gambo

Har ila yau kungiyar tana cigaba da neman mai koyarwa Alejandro Menedez Garcia, dan Sipaniya domin zama mai koyar da kungiyar a kokarin da kungiyar take na ganin tasamu nasara a kakar wasan da za’a fara a sati mai zuwa.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: