Dan Wasan Kano Pillars Rabiu Ali Ya Kai Nijeriya Wasan Karshe

Kwallon da dan wasan tsakiyar Kano Pillars, Rabiu Ali ya jefa a ragar kasar Benin ce a daidai minti goma da fara wasa ya sa tawagar ‘yan wasan Nijeriya masu buga wasan cikin gida suka kai wasan karshe na gasar cin kofin nahiyar Africa na ‘yan wasan da suke buga wasa a gida.

Wannan nasarar tasa NIjeriya za ta fafata da mai masaukin baki kasar Ghana bayan da ta doke Jamhuriyar Nijar da ci 2-0.

Kociyan tawagar ‘yan wasan Ghana Madwell Konadu ya ce ‘yan wasansa sun shirya domin doke NIjeriya a wasan karshen da za a fafata.

NIjeriya dai ta doke Ghana a wasan rukuni-rukuni a wasan karshe, sai dai kociyan na Ghana ya ce a wancan wasan wasu daga cikin ‘yan wasan kungiyar suna da ciwo amma yanzu kowa ya warke kuma za su doke ‘yan wasan na super eagles domin lashe gasar.

A ranar lahadi ne dai za a fafata wasan karshen a filin wasa na Cape Coast da misalin karfe bakwai na dare agogon NIjeriya bayan an buga wasan neman na uku tsakanin kasar Benin da Jamhuriyar Niger.

Exit mobile version