Dan Wasan Nijeriya Kilechi Iheanacho Ya Kafa Sabon Tarihi A Kasar Ingila

Dan wasan Najeriya da ke taka buga wasa a kungiyar kwallon kafa ta Leicester City, Kelechi Iheanacho ya zama dan wasa na farko da ya zura kwallon da fasahar bidiyon alkalanci ta amince da ita a kasar Ingila.

An fara amfani da wannan fasahar ce don taimaka wa alakalin wasa wajen yanke hukunci, yayin da Iheanacho ya fara zura kwallon farko da bidiyon ya amince da ita a fafatawar da kungiyarsa ta casa kungiyar Fleetwood da ci 2-0 a a gasar cin kofin kalubale na FA a ranar Talata..

A karo na uku kenan da ake gwajin wannan fasahar a Ingila, in da aka yi amfani da ita a fafatawar da Brighton ta yi da Crystal Palace da kuma karawar da Chelsea ta yi da Arsenal duk a cikin wannan watan na Janairu.

Tun farko dai alkalin wasan dayake alkalancin wasan yace kwallon bataci ba sakamakon cewa Iheanacho yayi satar gida amma daga baya na’urar wadda aka kirkira domin taimakawa alkalin wasa ta tabbatar da cewa dan wasan baiyi satar gida ba kuma yakamata alkalin wasa ya karbi kwallon.

Na’urar dai anyi ta ne domin ta dinga taimakawa alkalan wasa wajen halasta kwallon da akace bata ciba tun farko.

 

 

Exit mobile version