Connect with us

WASANNI

Dan Wasan Nijeriya Ya Lashe Kyautar Gwarzon Gidan Radio Faransa

Published

on

Dan wasan gaba na tawagar Super Eagles ta Najeriya, Bictor Osimhen, ya lashe kyautar gwarzon dan wasan Afirka na Marc-bibien Foé na shekarar 2020 a ranar Litinin kamar yadda gidan radio Faransa ya tabbatar.

Ita dai wannan gasar da ke dauke da sunan tsohon dan wasan Kamaru Marc – bibien Foé da ya gamu da ajalinsa a filin wasa a Faransa, hadin guiwar kafar Talabijin din France 24 da Radion France International RFI ke shiryata tun a shekarar 2011 kuma duk shekara domin karrama marigayi Foé.

Gasar da ke maida hankali kan bajinta da dan wasa ya nuna a gasar Ligue 1 na qasar Faransa, a wannan karon dan wasan Najeriya da ke buga qwallo a qungiyar qwallon qafa ta Lille ya yi nasarar lashe gasar bayan duke abokan karawarsa Islam Silimani dan qasar Algeria dake wasa a Monaco da kuma dan qasar Moroco Yunis Abdelhamid dake wasa a stade de Reims.

Bictor Osimhen ya kuma kafa tarihin mafi qarancin shekaru da ya taba lashe gasar, wato shekaru 21 kamar yadda tarihin lashe gasar ya nuna kuma hakan ya faru ne sakamakon bajintar da dan wasan ya nuna a wannan kakar da aka kammala a qasar ta Faransa.

Duk da tsaiko da annobar koronabirus ta haifar a sabgar ta wasanni, Bictor Osimhen ya zura qwallaye 13 sannan ya taimaka anci qwallo har sau 4 a wasanni 27 da ya buga a wannan kaka, abin da ya bashi damar lashe gasar da gagarumin rinjaye wato maki 284, inda abokan karawarsa suka samu maki 95 da kuma 89

Tuni dai hukumar gudanarwar qungiyar qwallon qafa ta Lille ta miqa saqon murna ga dan wasan nata wanda a daidai wannan lokacin qungiyoyin qwallon qafa da dama ciki har da Liberpool da Real Madrid da Napoli suke zawarci.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: