Sani Anwar" />

Dana Ya Na Nan A Raye – Tijjani Asase

Kamar yadda wasu kafafen yada labarai ke ta faman yada farfaganda cewa, an hallaka dan fitaccen Dan wasan Kwaikwayon nan, Tijjani Asase, wanda bai jima da kammala saukar Alkur’aninsa ba, ta hanyar kwace ma sa keken Adaidaita Sahu a jihar Kano, wannan ba gaskiya ba ne, illa shaci fadi kawai.

Mun samu wannan sanarwa ne daga shafin sadar da zumunta na daya daga cikin makusantan Tijjani Asasen, wato Mudassir Kasim, inda ya bayyana cewa, ya tuntubi Asasen don jin gaskiyar al’amarin dangane da wannan abin da ke faruwa, ya kuma yi ma sa bayani daki-daki kamar haka:

“Na bayar da cigiyar Babur din Adaidaita Sahu, wanda a ka sace wa wani dan’uwana, wanda yake kamar Da a wurina. A wajen bayar da wannan sanarwa, ko kadan ban ambaci sunan dana wanda ya yi saukar Alkur’ani a kwanakin baya ko wani abu mai kama da haka ba, amma kawai ni ma sai ji na yi na kuma gani a shafukan sada zumunta na Facebook, a na ta faman yada wannan farfaganda wadda ko kadan ba ta da asali ballantana tushe.”

Babban abin haushi da takaicin ma shi ne, yadda wasu Kafafen yada labarai wadanda mafiya yawansu al’umma na girmama labaransu tare da ba su muhimmaci, amma sai ga shi su ma sun buge da yayata irin wadannan labarai marasa tushe da kuma kan-gado kwata-kwata.

A karshe, Kasim ya ja hankali tare da baiwa irin wadannan kafafen yada labarai irin na kanzon kurege shawara musamman ta fuskar rika yin kokarin tantance labaran gaskiya kafin su kai ga fara yada shi a cikin al’umma ko irin wadannan kafafen yada labarai na zaurukan sadar da zumunta da sauran makamantansu, domin kuwa a cewar tasa, hakan babu abin da zai Haifa musu, illa zub da kima da kuma mutunci a idanun al’umma da kuma sauran wadanda ke saurare ko bibiyasu a irin wadannan zauruka.

Exit mobile version