Dandalin Facebook Da Harkallarsa

Daga Ibraheem El-Tafseer

 

Kafar sadarwa ta Facebook, daya ne daga cikin kafofin sadarwa na zamani wacce ake aika sakonni cikin gaggawa. Facebook, daya ne daga cikin ‘Applications’ (manhajoji) dangogi irin su Twitter, Instagram, Telegram, Snapchat da sauransu. Kamar a Nijeriya kam, Facebook ya fi shahara a yanzu, tun da an rufe kafar sadarwa ta Twitter.

Ana yi wa Facebook lakabi da kafar sada zumunta. Tun da a Facebook ana iya haduwa da mutanen da ba a sansu ba, kuma a kulla alaka mai karfi, har ta kai an ziyarci juna, daga nisan garuruwa. Facebook yana hada zumunci sosai, sannan yana raba zumunci sosan gaske.

Na san ba sabon abu bane, haduwa ta dalilin Facebook har a ziyarci juna daga nisan jihohi a fadin Nijeriya. Wannan ya sha faruwa, akwai dalilai da yawa kan haka. Kuma zumunci ya kullu yadda har idan wani abin farin ciki ko na bakin ciki ya faru da daya, su kan ziyarci juna. Facebook yana hada zumunci tsakanin namiji da mace har ya kai ga sun yi aure. Ni ma akwai abokina da dalilin Facebook suka hadu da matar da ya aura, kuma har yanzu suna tare. Facebook yana hada abubuwa da yawa ciki har da badala.

 

Akwai dandali da dama na sada zumunta da yawa a Facebook, wanda ya hada mutane da dama, maza da mata, ana kuma sadar da zumunta din. Misalin daya daga cikin irin wadannan dandalan shi ne dandalin ‘Home Of Solace’ wanda ko a watannin baya sun shirya taro, kuma da yawa daga cikin ‘yan dandalin sun halarta, an ci, an sha, an yi raha, sannan aka dauki hotuna. Zumunci ya kullu tsakanin da dama daga cikinsu.

 

Facebook wani wuri ne da mutane suke rubuta ra’ayoyinsu da nufin isar da sako, cikin harsunan da suke bukata sakon ya isa. Kamar mu a nan Nijeriya, an fi yin rubutun da yarukan Hausa, Turanci, Larabci da Faransanci. Da farko idan mutum ya bude shafin Facebook, akwai bukatar ya san da wane dalili ya bude shafin Facebook din. Idan sako yake so yana isarwa, to sai ya duba ya ga da wane yare ya kamata ya yi rubutu wajen isar da sakon, domin sakon ya isa ga wanda aka yi dominsu. Wasu suna hawa Facebook ne don su karanta labarai da sauransu. Wasu kuma suna hawa Facebook ne don su ci mutuncin wasu.

 

Akwai ‘Gidauniyoyi’ na neman taimako da yawa da suke aikawa da sako hotunan wadanda ake nema wa taimakon a shafukansu na Facebook. Kuma tabbas ana samun taimakon sosai a Facebook din. Akwai misalai da yawa kan haka. Hajiya Fauziyya D. Sulaiman daya ce daga cikinsu.

 

Facebook ya kasance wajen samun labarai cikin gaggawa. Kusan dukkan kafofin yada labarai na jaridu da gidajen Talabijin da Rediyo duk suna da shafi a Facebook wanda suke wallafa labaransu a ciki. Da zarar labari da dumi-dumi ya samu, za ka ga suna ta rige-rige wajen wallafa wa a shafukansu. Hakan ya sa mafi yawan labarai a Facebook ake fara gani, kafin a samu cikakken labarin daga baya. Facebook din kuma ya shahara wajen kawo labarai na kanzon kurege, shi ya sa da yawan mutane ba sa yarda da labaran Facebook, har sai sun ga wata jarida ta gaske ta wallafa labarin a shafinsu. Abin da ya sa na ce jarida ta gaske shi ne, jaridun bogi suna nan birjik a Facebook. Da zarar mutum ya sayi babbar waya, to shi ma ya zama dan jarida. Abin da yake ta faruwa kenan yanzu a Facebook da WhatsApp. Wasu kuwa suna hawa Facebook ne don ganin labaran ban dariya (comedy), don nishadi da rage damuwa. Wasu kuma fasadi kawai suke yada wa a Facebook. Ko kunya babu za ka ga suna ta furta kalaman batsa da rashin tarbiyya iri-iri a bidiyo su dora a Facebook da sunan tallan magani ko kuma yada iskanci.

 

Haka kuma Facebook ya zama wajen hada-hadar kasuwanci iri-iri. Kusan dukkan masu manyan masana’antu, da masu manyan shaguna har da masu matsakaitan kasuwanci, duk suna da shafuka da suke tallata harkokin kasuwancinsu ta hanyoyin rubuce-rubuce a Facebook, hade da hotuna da Bidiyon yadda kasuwancin nasu yake.

 

Sannan Facebook ya zama wajen sanar da sakonnin aure, suna da mutuwa. Zai wahala garin Allah ya waye, ba ka ga an sanar da daya daga cikin ukun nan ba. Dalilin Facebook ya sa an daina buga katin aure barkatai da ake yi a shekarun baya.

Facebook ya zama wajen yada manufofin ‘yan Siyasa. Kowace jam’iyya tana da nata shafin a Facebook domin yada manufofin ta. Duk wani babban dan siyasa yana da nasa yaran masu tallata manufofinsa da ayyukansa a Facebook.

 

Haka za ka yi ta kallon hotunan ‘yan Siyasa daga ko ina a fadin kasar nan. Wani daga an dora hotonsa rikici zai barke a wajen ‘comments’ a yi ta zage-zage da cin mutuncin juna. Mummunar gaba ta kullu tsakanin masoyan jam’iyyun, su kuma ‘yan siyasar babu ruwansu. Sai dai ma a nuno su sun hadu a wajen wani taro suna gaisawa da juna har suna dariya da raha.

Akwai kuma wadanda suka dauki Facebook tamkar makaranta, suna karuwa matuka da rubuce-rubucen da wasu suke yi, na addini da kuma masu yin sharhi kan al’amuran yau da kullum. Akwai wadanda kullum da ka ga rubutunsu a Facebook, to wa’azi ne ko nasiha. Irin wadannan su ne suka fi kadan.

 

Akwai wadanda suka dauki Facebook wajen cin mutuncin jama’a, su zagi wanda suke ki, su ci mutuncinsa, su bata masa suna, saboda wata manufa ko bambamcin fahimta na addini ko bambamcin ra’ayi na siyasa. Irin wannan shi ya fi yawa sosai a Facebook yanzu. Akwai wadanda suka daina bude shafinsu na Facebook saboda irin cin mutuncin da ake yi wa jama’a, musamman Malaman addini. Duk girman Malami za a iya kunduma masa ashar. A Facebook ne za ka ga an dauko hoton Malamin addini an jirkita masa kama an yi amfani da ‘Photoshop’ an nuna shi cikin wata mummunar kama, ko  kuma ma a nuna suffarsa hade da wata dabba. A Facebook ne za ka ga jahili, wanda bai taba shiga aji ba, yana kiran babban Malamin addini da jahili ko mahaukaci, saboda tsantsar kiyayya ko kuma sabanin fahimta.

 

A Facebook ne dan Sakandire zai kira Malamin da ya yi digirin digirgir (PhD) da jahili, saboda bambamcin ra’ayi. A Facebook sam wasu ba sa ganin kima da darajar mutane, ko waye za su iya ci masa mutunci, su kunduma masa ashar.

A Facebook ne saboda ana bukatar a bakanta mutum, musamman Malaman addini, sai a dauki tsoffin jawabansa da sabbi a yayyanke, a jojjona inda ake so, don fitar da wata mummunar manufa, don a bata masa suna, ya faru da yawa mun gani.

Facebook ya zama wajen yada karerayi, kazafi, kage da sharri. Akwai wadanda suka daukar wa kansu haka, kullum abin da suke yada wa kenan a Facebook. A Facebook ne ake kirkirar labarin da babu shi, kuma a yi ta yada shi, sai daga baya a gano labarin bashi da asali ballantana tushe. Labarin kanzon kurege kam ya zama ruwan dare a Facebook. Ko a makon da ya gabata, an yi ta yada cewa tsohon ministan wutar Lantarki, Saleh Mamman wai ya yanki jiki ya fadi, a lokacin da ya samu labarin an tsige shi. Da ‘yan Jarida suke tambayarsa kan haka, sai ya ce shi ma a Facebook ya gani ana ta yada wa, amma karya ake masa, shi kam bai fadi ba. Shi ma bai san daga ina labarin ya samo asali ba.

 

A Facebook din nan dai za ka ga Hausawa, ‘ya’yan musulmai suna dora hotunansu, wanda bashi da maraba da tsirara, suna tallata kansu ga jama’a. Abin mamakin sai ka ga wasu maza masu irin budurwar zuciya din nan, suna ta yaba musu hotunan, su kuma suna jin dadi. Wanda hakan ya saba da koyarwar addinin Musulunci da kuma al’adar Bahaushe.

 

Yadda wasu suke rubuta abin da suka ga dama a Facebook, da sunan ‘yancin fadin albarkacin baki (Freedom of Edpression). Su zagi wanda suke ki, su yi karya, kage da kazafi ga wasu mutanen da suke da bambamcin fahimta a addini ko a siyasa. Wasu iyayen gidansu ne suke saka su, wasu kuma ra’ayin kansu ne. To yana da kyau mutum ya sani, a duk lokacin da za ka yi rubutu a Facebook ko kuma rubutu a ko ina, to ka tuna cewa Allah zai tambaye ka a kan wannan rubutun. Duk abin da ka rubuta, Allah zai tayar da kai, a ranar Lahira, ya maka tambaya a kan abin da ka rubuta. Lallai a yi taka tsantsan wajen rubuta abin da mutum ya san ba gaskiya bane.

El-Tafseer, ana iya samu na a email ta: eltafseerpen@gmail.com 

Exit mobile version