Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home ADABI

Dandawo Ya Dawo!

by Tayo Adelaja
September 17, 2017
in ADABI
5 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Alhaji Sani Aliyu Dandawo ya rasu a ranar 4 ga Afrilu, 2016, inda ba mutanen yankinsu na Yawuri kaDai su ka yi alhini da jimamin mutuwar, Alhaji Sani ba, a’a, kowanne bangare na kasar Hausa sun shiga damuwa ko dai don kasancewarsa makusanci da kyakkyawar mu’amalarsa ko kuma sun shiga damuwa ganin ko shakka babu wani bango ya faDi a bangaren raya al’adun fada ta hanyar waka, inda su ke fargabar kasar Hausa ba za ta iya sake maye gurbinsa ba. To, amma shekara guda bayan rasuwarsa wannan mashahurin mawaki, kwatsam! sai ga Dandawo ya dawo.

Masu iya magana sun ce kyan Da ya gaji gidansu. Cikin ikon Allah Dan Alhaji Sani Aliyu Dandawo na cikinsa mai suna Ibrahim Dandawo ya fara waka da kafar dama, musamman da ya ke Allah Ya tarfawa garinsa nono; indai ta murya ko fasaha ne, to kuwa ka ce kamar kwabo da kwabo, wato dai kasar fago ta mayar da fago. Yanzu haka wannan mawaki har manyan sarakunan Arewa sun fara jan sa a jika, don ya yi mu su wakoki, kamar yadda a kan mahaifinsa a kai. Wakiliyar LEADERSHIP A YAU LAHADI, Bilkisu Yusif Ali, ta yi katarin tattauna wa Ibrahim Sani Aliyu Dandawo. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

samndaads

Za mu so ka ba wa masu karatu tarihinka a takaice.

Ni Alhaji Ibrahim Sani Dandawo an haife ni a garin Yauri ta jihar Kebbi a shekarar 1970. Na fara da karatun Alkur’ani kamar yadda ya ke a al’adun Hausawa, kuma kamar yadda Musulunci ya yi umarni, har zuwa lokacin da na tasa a ka sa ni a makarantar firamare ta garin Yauri. Bayan na kammala na tafi sakandire ta JSS Koko har zuwa 1981, inda na koma GSS Yauri na kammala a 1987. Daga nan na wuce Polytechnic ta Kebbi, inda na yi difloma da HND. Ina da aure da yara. Yanzu haka ni ma’aikacin hukumar kula da shige da fice ta kasa (Immagireshin) ne.

Gaskiya ni ban koyi waka a wajen mahaifina ba. Bilhasali ma shi ba ya son mu yi waka. Don haka ya Dora mu a kan karatu kuma duk karatun mu ka yi. A lokacin ya kawo min dalilai guda biyu. Na farko, ya na ganin al’adun Hausa sun fara tabarbarewa. Yadda a ke martaba makaDan a baya musamman makaDin fada, kullum abin ya na ja baya ne. Sannan a wancan lokacin sarakuna ke Daukar duk larurar makaDinsu da jama’arsa; ci da sha da sutura da duk wani abu da zai gitta na yau da kullum, amma daga baya sai wannan Dawainiya ta ke ja baya. Mu kuwa wakokin sarauta mu ke yi. Sai tunanin ko da ka dogara da wakar, ba za ta ishe ka Dawainiyar yau ba. Don haka ba Dansa da ya koyawa waka ko ya Dora shi ma a kan waka.

To, ya a ka haihu a ragaya?

(Dariya) To, ni ma dai ban san lokacin da na iya waka ba tunda ni ban koya ba. Kawai dai na ga Ina waka. Don haka har yanzu na ke ji a jikina ban iya ba. Amma a lokacin da Maigida ya na da rai, ya kan Dan tura ni na wakilce shi a bikin sarauta, musamman akwai wata al’ada da mu ke cewa Cin Goro, wadda a ke yin ta bayan kwana Daya da sallah da raka sarki bayan an taso daga Idi. Amma ko wannan Din sai in ba shi da lafiya kuma ko a wancan lokacin wakokinsa ne na ke yi. Amma akwai wani lokaci, zai kai shekara goma baya lokacin shugaban kasa Olusegun Obasonjo, an ba wa Sarkin Yauri lambar girmamawa ta kasa (CON) a ka karrama shi a Abuja kuma a daidai wannan lokacin Maigida ya sami tsautsayi ya karye. Don haka ya umarce ni na yi waka a wajen. Ko da yake a wannan lokacin ba wakarsa na yi ba, to amma shi ya ba ni kan wakar, amma Diyan wakar nawa ne.

Yaushe ka fara yin waka taka ta kanka?

Wakata ta farko na yi ta ne tun mahaifina ya na da rai, amma ba shi da lafiya a 2014. Sai kuma bayan rasuwarsa, da ya ke lokacin ba nisa da sallah, ni na yi wasa a gidan sarki. Wannan sallar ita ce karo na huDu da na yi wasa a sallah.

Kai ma za ka takaitu ne a fada, kamar mahaifinka?

Eh to, duk da ni makaDin fada ne, kamar mahaifina, wannan bai hana mu yi wa wani waka ba duk wanda ya bukata. Ya dai danganta, amma dai mu wakokinmu mun takaita inda za mu je mu yi waka sai ko a naDin sarauta ko wajen bikin aure ko wata kungiya ko wani taro na shari’a. Amma ba za a gan mu a wani waje wanda ya sabawa al’adunmu da addininmu ba ko inda mutuncinmu zai zube ba. Amma har zuwa yau wakokina daga saraki sai ko ’ya’yan sarki na yiwa.

Duk gadarsu na yi daga wajen maigida. Ai sake ’yan amshi ba abu ne mai sauki ba, saboda za a Dau tsahon shekaru kafin a ce sun iya. Allah na horewa kowa fasaha, amma da wuya, saboda waka ce wadda ta ke Dauke da karbi da kari su na Dora wakar abu ne da sai an shirya sosai.

Me ya ja hankalinka ka fara waka?

Ni tun farkon tasowata Ina da sha’awar waka, saboda gidanmu waka mu ka gada. Don haka Ina kishin gidanmu, sannan al’adunmu a bangaren kiDa da waka sun tasamma rushewa. Babban kalubalen shi ne yadda manyan wakan su ke rasa magada masu azama wanda kuwa in har an tafi a haka wata rana za a nemi waka irin tamu ta gargajiya a rasa musamman kiDan fada. Sababbin mawaka kuma da mu ke da su yanzu ba sa yin abin a gargajiyance. Sun aro kayan kiDan Turawa su na amfani da su. Wani dalilin kuma na Dauki waka saboda saurin isar da sako. Amma ni ban Dauki waka sana’a ba ko wata hanya ta neman kuDi. In an ba mu mu gode, in ma ba a ba mu ba ma ba za mu daina waka ba. Haka in mun yi waka ba ma recording. Kai wanda a ka yi wa kai za ka naDi kayanka, sannan masu sana’ar saida cd su ma in sun Dauka ba ruwanmu; su je su sayar su ci abinci. Kamar yadda Alhaji Sani ya faDa a lokacin Marigayi Sarki Shu’aibu:

Allah ji kan Kangiwa Shehu

Domin shi yas sa ni ga hanya

Ya ce mi ni Mamman Sani

Mamman dawo kama sana’a

In Allah Ya so Ya yarda

Mu za mu taimaka ma ka kullum

In waka ta samu ka yi ta

In ba ta samu ba ka yi ta sana’a

Mene ne fatanka wajen al’umma?

Babban fatana shi ne yadda su ke da kamfar mawaka irin na dauri su ke da shaukin son a raya al’adunmu, to su ba mu goyon baya. Ina gode wa masoyana da yi mu su kyakkyawan fata, saboda masu kauna ta a yau su na yi min ne saboda mahaifina. Alhaji Sani Aliyu Dandawo ya rasu mutane da yawa ba su san Dansa yanzu ya na waka ba. Ta hanyar yayatawa ne za a ji. Don haka al’umma sai sun tallafa sakon zai isa kunnuwan masoya.

Leadership A Yau na godiya.

Ni ma na gode kwarai da gaske.

SendShareTweetShare
Previous Post

Labarin Tsohuwar Daular Musulunci Ta Andulus

Next Post

Asalin Rubutun Hausar Boko Da Bunkasar Harshen Hausa

RelatedPosts

Fitattun Littattafan Hausa A 2020

Fitattun Littattafan Hausa A 2020

by Sulaiman Ibrahim
6 days ago
0

Masu iya magana suka ce 'komai ya yi farko zai...

Rayuwan Aurena

Sharhin Littafin: A Rayuwar Aurena: Abin Da Ba Zan Manta Da Shi Ba

by Muhammad
2 weeks ago
0

Na Adamun Adamawa Bauchi Daga Yusuf Kabir 09063281016 Sunan wannan...

Zama Farfesa

Ina Son Zama Farfesa, Cewar ’Yar Shekara 18 Da Ta Wallafa Littafi A Kebbi

by Sulaiman Ibrahim
3 weeks ago
0

MAIMUNA GARBA HAMMANI wata matsashiyyar yarinya ce ’yar Shekaru 18...

Next Post

Asalin Rubutun Hausar Boko Da Bunkasar Harshen Hausa

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version