Tare da Rukayya Ayyuba Adamu
Lokaci ya kawo mu, yayin komawar yaran mu makaranta.Tabbas kowacce uwa tana ta kokarin tabbatar da cewar ’ya’yanta sun shiga sabon aji, domin fuskantar zangon karatu na gaba. Babban burin duk wata uwa game da danta, shi ne ganin yana samun ci gaba ta fannin girmansa na jiki da kuma samun nasara musamman ma a bangaren karatu. Abubuwan da suka kamace mu a matsayin mu na iyaye mata, mu tabbar game da shirye-shiryen komawar ’ya’yanmu makaranta sun hada da:
Kiwon lafiyar yaranmu, su zama cike da koshin lafiya a yayin da lokacin komawa makaranta ya yi na da muhimmanci. Domin lafiya uwar jiki, hakan ne kadai zai ba su damar yin azama da zama masu fahimta a wajen fara daukar darasi a makaranta. Idan kuma yaro ya kasance ba shi da lafiya a lokacin komawa makaranta, yana da kyau a sanar da hukumar makarantar sannan da zarar ya samu sauki a yi kokarin ci gaba da shirya shi domin ya halarce ta.
Ya kamata mu duba zukatan ‘ya’yanmu dangane da yadda suka dauki darajar neman ilimi. Mu shirya su domin tunkarar kalubalen da ke tattare da haduwa da sababbin darussa. A inda muka samesu da raunin tunani game da kalubalen karatu na zangon karatu da ya gabata, sai mu gyara musu tunaninsu mu kuma basu kwarin gwiwa.
Suturar da za su yi amfani da ita, mu tabbatar ta na da yalwa ba ta yi musu kadan ba, sannan idan akwai hali a kara dinka musu sababbi domin hakan yana taimakawa yaro wajen kyautata tunaninshi game da darajar sa, kuma hakan zai taimaka mishi wajen samun kwarin gwiwar tunkarar sa’o’inshi a aji da wajen wasannin motsa jiki na makarantar. Wandon yara yana daya daga cikin suturar da ke saurin dagewa yaro a duk lokacin da aka koma sabon zangon karatu. To a nan sai mu yi dabarar yi mishi kari daga saman zariyar wandon, domin ya kara tsayi ko kuma mu warware mishi kasan wandon musamman ma idan tela ya bar alawus a wajen kalmasar shi.
’Ya’yanmu mata ya kamata su koma makaranta da sabon kitso. Kuma mu tabbatar kafin a yi mu su kitson an tsaftace mu su gashinsu. Maza kuma a yi mu su aski. A al’adance idan akwai wani sha’ani da aka yi gab da komawar yara makaranta to, gaskiya bai kamata a bari ‘yammata su yi kunshi ba domin sau dayawa dokar makaranta ba ta amince dalibai su je makaranta da kunshin ba, musamman ma mai dauke da zanen fulawoyi ko ja ko baki.
Idan mu ka yi la’akari da yanayin lokacin da mu ke za mu ga cewar ruwan sama bai daukeba kwata-kwata. Saboda haka yana da muhimmanci a ce yaranmu suna da rigunan ruwa ko lema domin kada a rinka samun tsaiko ko fashi a yayin da aka fara karatu gadan – gadan a makaranta.
Wani muhimmin abu kuma shi ne tsarin tanadin abincin da yaranmu zasu ci a makaranta. Dole ne mu tsara wani jadawali wanda da shi ne za mu rinka samun jagoranci wajen wannan tsari domin samun dorewa a lafiyarsu da muka dade muna kiwo. Masana tsarin cin abinci yadda ya kamata sun yi wani binciken da ya tabbatar da cewa mafi akasarin iyaye suna raja’a ne da siyawa yaransu biskit da lemon kwalba ko na kwali ko na roba a matsayin abincin da za su ci a makaranta. To amman ita uwar da ta san muhimmancin kulawa da lafiyar iyalinta ba ta daukar wannan tsari da ganin zai haifar mata da da mai ido. Saboda hakan ta na kokarin ganin ta yi amfani da baiwar da ta ke da ita wajen sarrafa abubuwan da danta zai ci mai dauke da abubauwan da su ke gina jiki da kulawa da lafiya. Misali kamar irin su kayan marmari da ganye da kuma hatsi mai kara wa jiki lafiya da kuzari.
Akwai wata dabi’a da sai mun gyara game da tanadin karin kumallon ‘ya’yanmu kafin su tafi makaranta. Domin kuwa hakan yana da muhimmanci kwarai da gaske. Mafi akasarin ‘ya’yanmu muna shirya su ne da gaggawa domin gudun kar su kai ga makara. To amman wane irin abinci ya fi dacewa su ci a irin wannan yanayin, abu ne da ya ke bukatar nutsuwa da tunani. Idan kuwa ba haka ba to za mu ga yaranmu duk sun rame sun fita hayyacinsu a cikin dan kankanin lokaci bayan komawa makaranta. Saboda sau dayawa abincin da mu kan saka musu a jaka su tafi haka suke dawo mana das hi ba su ci ba.
A tanadin kayan rubutu akwai: Biro da Fensira da kilina da shafina da reza da almakashi da rula da caloli, da takardar zane. Daga cikin wadansu muhimman abubuwa akwai: Robar ruwa da kwanon abinci da jakar da za a sa kayan abinci a ciki da lema ko rigar ruwa da hankaci da safa da takalma na zuwa aji da na wasan motsa jiki.