Connect with us

Uncategorized

Dangane Da Siyawa Shugabanni Fom

Published

on

Niccolo Bernardo Machiabelli wani masanin siyasar Turai ne ya yi zamani tsakanin shekarun (1467-1527) an haife shi kuma ya rayu a birnin Florence na kasar Italiya, ya kware a fannin amfani da karfin soja da kuma dabarun siyasa wajen cim ma manufa. Ya rubuta littafi mai suna THE PRINCE wanda a cikinsa shawawari ne da ya bai wa shugaban kasar ta Italiya lokacin yana Sakatare na biyu ga Chancery. A nazarin siyasar Machiabelli yana da ra’ayin cewa shugabanci da kuma mutuntaka wasu ababe ne mabambanta.

Mutuntaka kamar yadda ya ce tana da amfani ne a wurin shugaba idan za ta taimaka masa wajen bunkasa mulkinsa. A wurinsa babu mutuntaka wajen amfani da iko sannan babu mutuntaka wajen gwagwarmayar neman mulki, sannan bai kamata shugaba ya dinga duba mutuntakarsa wajen tafiyar da mulkinsa ba. Saboda haka abin da littafin na Machiabelli ya ba da karfi shi ne hanyoyin yaudara da damfara da mutum zai bi ya samu mulki, da idan ya samu mulkin hanyoyin da zai bi ya tabbatar da mulkin, sannan kuma yadda zai bunkasa shi mulkin nasa. Kundi ne da ‘yan siyasa suka dau tsawon lokaci suna amfani da shi. A cewarsa shugaba mai yaudara  kowanne lokaci yana samun wadanda za su yarda ya yaudare su.

Bisa ga dukkan alamu wannan tunani na Machiabelli shi ne salon siyasar da masu rike da ikon gwamnatocin yau suka fito da shi wajen sake yaudarar talakawa ta hanyar nuna musu ba su da ko kudin siyan fom saboda gwamnatinsu mai gaskiya ce. Shekaru uku ke nan da zaben wannan gwamnati, wanda idan aka dunkule dalilin da ya sa aka taru aka zabi gwamnatin bai wuce dalilai guda uku ba. Na farko inganta rayuwar dan kasa musamman talaka, na biyu kawo gyara da bunkasa tattalin arzikin kasa na karshen kuma kyautata tsaro. Sai dai shin bukatar ‘yan kasa ta biya?

Na taba jin wani mutum yana cewa da zarar shugaba Buhari ya karbi mulki daga ran nan duk wata matsala ta wuce a kasar nan, saboda kyautata za ton da yake yi masa. Kamar yadda yake fada Buhari ne kadai ya san abin da yake damun kasar, shi ne kuma ya san hanyoyin da zai  gyarata. Wannan irin fata da mutane suke da shi ga gwamnatin ne  ya sa suka ta yi mata uzuri a bangarori da ake ganin ta gaza.

Domin kuwa, babu abin da ‘yan Nijeriya suke da  bukata kamar shugabancin da zai fitar da su daga cikin ha’u la in da suke ciki. Hasali ma dai bukatarsu da shugabancin ne ya kai su shiga jirgin canji. To amma dai bisa dukkan alamu har yanzu garin wannan canji da nisa ga akasarin talakawan Nijeriya.

Canji da ‘yan Nijeriya suka yi fata bai wuce idan a da shugabanni suna karya to shugabannin gwamnatin canji su zama suna fadin gaskiya. Idan aka samu haka an samu canji a magana. Idan shugabannin da suna fifita bukatar kansu a kan ta ‘yan kasa, sai gwamnatin canji ta zama ta fifita bukatar mutanen da suka zabe ta fiye da ta su bukatar ta kashin kansu. Idan shugabancin da ya gabata ya ki mutunta doka shugabannin canji su kuma su mutunta.

Idan shugabanin baya an kawar da su saboda nuna wariya da son kai a mulki da tsunduma  ‘yan uwansu da danginsu da kabilarsu cikin sha’anin mulki da ba su mukamai domin cim ma manufar siyasa. Canji shi ne gwamnati da ta zo da canji a ga sabanin haka a tattare da ita, ta yadda za ta rungumi kowa kamar yadda dokar kasa ta ce. Ko ma kamar yadda gwamnatin ta rantse za ta yi. Idan cikin abin da a ke zargin shugabannin baya shi ne lalata bangaren ilimi da kuma tura ‘ya’yansu waje karatu da yin biris da mawuyacin halin da jami’o’in kasarnan suke ciki. To su a ga sun ba da himma wajen farfado da su ba wai su ma su ketarar da ‘ya’yan na su waje ba.

Idan shugabannin baya sun bar asibitoci a lalace babu kayan aiki da ma’aikata balle magani ta yadda da zarar kan su ko kunnensu yana ciwo za su fita waje neman magani. Ya kamata a ga sabanin haka a gwamnatin canji. Shakka babu idan a ka rasa wadannan abubuwa a gwamnatin canji to al’amarin zai koma tsattsaman kunu a sabon koko.

Idan abin mu nazarci canjin da aka yi a kasar Cuba ne mu kwatanta shi da na Nijeriya za mu ga bambanci. Cuba da kasa ce matalauciya  ba ma kamar Nijeriya ba da muke da dimbim arzikin da ba mu san adadinsa ba. Ba ta da wasu abubuwa na tattalin arziki saboda danniyar kasashe irin su Amurka. Cuba koma baya ce a ilimi, koma baya ce a tattalin arziki, koma baya ce a fannin kiwon lafiya sannan koma baya ce a tsaro. Amma sakamakon juyin da Fidel Castro ya jagoranta yau kasar tana cikin kasashe masu kyakkyawan tsarin ilimi da kiwon lafiya a duniya. Hasali ma dai a yanzu haka tana taimaka wa wasu kasashe na duniya da likitoci da malaman makaranta. Dalibai daga sassa daban-daban na duniya suna zuwa jami’o’in kasar suna karatun fannin lafiya.

Ina iya tuna wa lokacin da ina jami’a, akwai wata daliba da ake tsokanarta da mai tafiyar ‘yan gayu. Saboda irin yanayin tafiyar da take da daman dalibai sun za ci cewa shakara ce irin ta ‘yan matan jami’a. Wata rana na je ofis din sashen da nake karatu sai na hadu da wannan daliba ta zo da takardar sanarwar cewa ko da wani abu zai taso za ta yi tafiya zuwa Cuba. A nan ne take shaida mini cewa wannan tafiyar da ake tsokanarta a kai ba wai da son ranta take yi ba. Ta ce ta yi hadarin mota ne har kafarta ta yi buguwar da ba za a iya gyarata a Nijeriya ba, shi ne aka dauke ta zuwa Cuba, to yanzu lokacin da likitocinta na Cuban suka dauka mata ta koma a cire wasu karafa daga kafarta ya yi shi ne za ta tafi.

Shi Castro an fara ganin canjin daga gare shi ne ta yadda abin da yake fada kuma ya kira mutane a kai shi yake aikata wa. Yana rayuwa irin ta talakawan kasarsa, wanda idan ya ce ma ka yau ba shi da kudi da gaske kowa ya yarda ba shi da kudin. Wannan dabi’a ta mutuntaka sabanin mutuntaka ta bukata ta Machiabelli da ma fi yawan ‘yan siyasar yau suke yi shi ya bai wa Castro nasarar mamayar zuciyar ‘yan kasarsa na tsawon lokaci.

Castro yana shugaban kasa amma yakan kutsa ya tattauna da mutanensa da ke cikin kauyuka, da dazuzzuka da kuma tsaunukan kasarsa a mota kirar jeep ba tare da rakiyar gayyar jami’an tsaro ba.

Mu dawo kan maganar siyawa shugabanni fom wanda shi ne ya kai mu ga wannan dogon surutun. Yanzu abin har ya zama gasa, kodayake da ma haka abin yake a gwamnatin. Daga wannan gwamna ya ce an siya masa, sai waccan ya ce ba shi da kudi amma sai da ya siyar da gidansa ya samu kudin siyan fom. Wannan salon ba zai kara tasirin wadannan shugabanni a zuciyar mutanen kasa ba.

Abin da ake bukata a gani a kasa wanda idan ta tabbata an yi maganinsu to shakka babu mutane za su yarda da gaske ne wadanda suka sayi fom din sun siya ne da kashin kansu ba wai Babarodo ba ne.

 
Advertisement

labarai