Jaridar Blueprints ta Nijeriya, ta wallafa wani sharhi da Dr. Agaba Halidu, na tsangayar nazarin kimiyyar siyasa da dangantakar kasashen waje ta jami’ar Abuja ya rubuta, mai taken “Waiwaye kan dangantakar Sin da Nijeriya cikin shekaru 50 da suka gabata”.
Cikin sharhin, Dr. Agaba Halidu ya yi ammana cewa, tun bayan kulla huldar diflomasiyya tsakanin kasashen biyu a shekarar 1971, sun yi mu’amala mai zurfi tare da zurfafa aminci a tsakaninsu. Ya ce Nijeriya na matukar goyon bayan aiwatar da manufar “Kasa daya mai tsarin mulki biyu” a kasar Sin. Sannan Sin, na karfafa hadin gwiwa da Nijeriya wajen harba tauraron dan Adam da kuma sauran wasu bangarori.
Ya ce tun bayan kafa dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afrika wato FOCAC a shekarar 2000, Nijeriya da Sin ke ci gaba da karfafa dangantakarsu bisa ka’idojin daidaito da girmamawa da moriyar juna, kuma dangantakar ta su na ta kyautata. Marubucin ya kara da cewa, a farkon shekarar nan, mamban majalisar gudanarwar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar, Wang Yi, ya samu nasarar ziyartar Nijeriya, inda ya kara karfafa dangantakar kasashen biyu.
Har ila yau, Sharhin ya nuna cewa, bangaren tattalin arziki ne jigon dangantakar kasashen biyu. Inda ya ce a shekarar 2018, yawan cinikayya tsakanin kasashen biyu ya kai dala biliyan 15.3. A shekarar 2019 kuma, jarin kai tsaye na kasar Sin a Nijeriya, ya kai dala miliyan 123.27. A yanzu haka kuma, sama da kamfanonin Sin 200 na gudanar da harkokinsu a Nijeriya. Ya kara da cewa, Nijeriya ta amfana da jerin manyan ayyuka masu inganci da Sin ta aiwatar, kamar layin dogo tsakanin Abuja da Kaduna, da layin dogo na cikin birnin Abuja, da yankin cinikayya cikin ‘yanci na Ogun da Guangdong da tashar lantarki ta Zungeru. Baya ga haka, sharhin ya kuma bayyana cewa, ana samun ingantuwar dangantaka da musaya tsakanin kasashen biyu a bangarorin al’adu da ilimi da ayyukan soji. Bugu da kari, Dr. Agaba Halidu ya yi imanin cewa, za a samu karin manyan sakamako karkashin dangantakar kasashen biyu a nan gaba. (Fa’iza Mustapha daga sashen Hausa na CRI)