Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
ADVERTISEMENT
Home JAKAR MAGORI

Dangi Sun Lakada Wa Wata Malamar Makaranta Dukan Kawo Wuka

by Muhammad
April 1, 2021
in JAKAR MAGORI
3 min read
Dukan
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Rabiu Ali Indabawa,

Wata malama a makarantar ‘Comforter City International School, Pakuro,’ da ke Yankin Karamar Hukumar Obafemi Owode ta Jihar Ogun, Grace Akinoso, na kwance a asibiti bayan da wasu ‘yan uwan ​​wani dalibi mai suna James Efeniye suka yi mata taron dangi suka lakada mata duka a harabar makarantar.

Jaridar PUNCH Metro ta tattaro cewa an kaiwa Grace hari ne saboda amfani da wayarta don yin faifan bidiyo na mahaifin James da kannensa biyu, Ezekiel da Samuel, yayin da ake zarginsa da cin zarafin wani dan bautar kasa, mai suna Jeremiah.

An ce Jeremiah ya ladabtar da James saboda rashin da’a yayin taron da malamai ke yi da dalibai, ‘Assembly’ amma wani dan’uwansa, Hebrew, ya yi sauri ya fita daga makarantar don ya sanar da iyayensu.

Yayin wata ziyara a makarantar a ranar Talata, daya daga cikin malaman, Sarah Orimisan, ta fadawa jaridar PUNCH Metro cewa mahaifin James ana zargin ya mari dan bautan kasar lokacin da ya isa makarantar.

Ta ce, “A yayin taron da safiyar yau, Jeremiah yana gargadin dalibi, James Efeniye da ya nuna halin kirki ya daina nuna dabi’a ta rashin da’a. Amma kawai sai ya fara takama yana jiji da kai, ya ci gaba da yin fahariya; saboda haushi, Jeremiah ya sami sanda ya yi masa bulala.” “Na umurci James ya durkusa na gargade shi da ya daina nuna halayya ta fahariya irin wannan.

Ya ce mai kula da makarantar ya mare shi a fuska jiya kuma Jeremiah ya yi masa magana a ranar (Talata), sannan na gaya masa cewa malamansa suna da ‘yancin yin hakan idan ya nuna musu wata dabi’a mara kyau.

“Na tambaye shi abin da ya aikata wanda ya sa Misis Ajayi ta doke shi, sai ya ce ya gaya mata cewa ba ya son ganin wawan hannunta da ke rubuce a allo. Kawai sai ya dauki jakarsa wai yana shi gida zai tafi na gaya masa ya koma ajinsa.

Daga baya na ji cewa ai ya yi tafiyarsa gida zai kira mahaifinsa. Jim kadan sai ga mahaifin nasa sun zo makarantar tare da manyan ‘ya’yansa maza biyu, Ezekiel da Samuel. Nan da nan mahaifin ya shiga makarantar, ya tafi ya sami Jeremiah ya kantsa masa mari. “Lokacin da Ezekiel da Samuel, tagwaye da James duk suka samu shiga alfarmar mahaifinsu, da mahaifiyarsu da wata mai yi musu hidima, sai suka wuce zuwa wajen shugaban makaranta suna neman a biya su kudaden makaranta da suka biya na‘ya’yansu. Sun kuma nemi faifan bidiyon da aka nada yayin da suke cin mutuncin dan bautar.

Suka shiga hargitsa ajujuwan makarantar, daga nan suka fara afkawa wata malama tamu, mai suna Grace, wacce ita ce dauki bidiyon, suna dukanta har ta yanke jiki ta fadi nan take. Dole muka garzaya da Grace zuwa asibitin Layo, inda a halin yanzu take jinya.”

Lokacin da jaridar PUNCH Metro ta ziyarci asibitin, an ganta Grace kwance a gadon asibiti ana yi mata karin ruwa. Ta fada wa wakilinmu cewa kaduwar harin ne ya haddasa faduwarta kwatsam.

An bayyana cewa, an kai rahoton faruwar lamarin a ofishin ’yan sanda na Mowe, inda aka kai ‘yan sanda zuwa wurin da abin ya faru.

Lokacin da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na ’yan sanda na jihar, Abimbola Oyeyemi, ya tabbatar da faruwar lamarin.

“Yaron, wanda ake zargi da cin zarafin matar, an kama shi kuma yana nan a tsare. An kuma kama mahaifin amma an ba shi izinin kula da kudaden kulawar yarinyar, wanda har yanzu tana asibiti. Shugaban makarantar ya sanar da ‘yan sanda faruwar lamarin kuma ana ci gaba da bincike,” in ji shi.

 

 

SendShareTweetShare
Previous Post

Matashi Ya Daba Wa Wani Wuka Har Lahira A Walimar Aure

Next Post

Manoman Shinkafa 44,000 Daga Rukuni 11 Suka Samu Tallafin CBN A Kano

RelatedPosts

Wiwi

NDLEA Ta Cafke Masu Fataucin Mutane Da Kwayoyi Na Naira Miliyan 564 A Abuja

by Muhammad
1 week ago
0

Babafemi ya ce wanda ake zargin mai shekaru 40 da...

kama

Yadda Danuwana Ya Tilasta Min Aikata Miyagun Laifuka –Wanda Ake Zargi

by Muhammad
1 week ago
0

A ranar Litinin Rundunar yan sandan karkashin jagorancin DCP Abbaa...

An Haifi Wani Yaro Da Azzakari Uku A Irak

An Haifi Wani Yaro Da Azzakari Uku A Irak

by Muhammad
1 week ago
0

Likitoci a Iraki sun bayar da rahoton haihuwar wani jariri...

Next Post
Shinkafa

Manoman Shinkafa 44,000 Daga Rukuni 11 Suka Samu Tallafin CBN A Kano

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version