Ministan Matasa da Bunkasa Harkokin Wasanni, Sunday Dare, ya bayyana cewa shahararren Dan kasuwar nan na Nijeriya, Aliko Dangote, zai gyara Filin Wasa na MKO Abiola dake Abuja.
Ministan ya ce, muna sa ran daga nan zuwa watan Maris, za mu samu manyan filayen wasa guda hudu masu dake da na’urori na zamani da Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya (FIFA) ta amince da su.
“Kuma ina tsammanin nan da wani dan lokaci takaitacce wannan kasar na iya amsar bakuncin kowane irin wasan kwallon kafa na FIFA.” in ji shi.